نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4890 | 54 | 44 | أم يقولون نحن جميع منتصر |
| | | Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?" |
|
4891 | 54 | 45 | سيهزم الجمع ويولون الدبر |
| | | Zã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu. |
|
4892 | 54 | 46 | بل الساعة موعدهم والساعة أدهى وأمر |
| | | Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci. |
|
4893 | 54 | 47 | إن المجرمين في ضلال وسعر |
| | | Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka. |
|
4894 | 54 | 48 | يوم يسحبون في النار على وجوههم ذوقوا مس سقر |
| | | Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar." |
|
4895 | 54 | 49 | إنا كل شيء خلقناه بقدر |
| | | Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri. |
|
4896 | 54 | 50 | وما أمرنا إلا واحدة كلمح بالبصر |
| | | Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido. |
|
4897 | 54 | 51 | ولقد أهلكنا أشياعكم فهل من مدكر |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni? |
|
4898 | 54 | 52 | وكل شيء فعلوه في الزبر |
| | | Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai. |
|
4899 | 54 | 53 | وكل صغير وكبير مستطر |
| | | Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne. |
|