نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4455 | 44 | 41 | يوم لا يغني مولى عن مولى شيئا ولا هم ينصرون |
| | | Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba. |
|
4456 | 44 | 42 | إلا من رحم الله إنه هو العزيز الرحيم |
| | | fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. |
|
4457 | 44 | 43 | إن شجرت الزقوم |
| | | Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã), |
|
4458 | 44 | 44 | طعام الأثيم |
| | | Ita ce abincin mai laifi. |
|
4459 | 44 | 45 | كالمهل يغلي في البطون |
| | | Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna. |
|
4460 | 44 | 46 | كغلي الحميم |
| | | Kamar tafasar ruwan zãfi. |
|
4461 | 44 | 47 | خذوه فاعتلوه إلى سواء الجحيم |
| | | (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm." |
|
4462 | 44 | 48 | ثم صبوا فوق رأسه من عذاب الحميم |
| | | "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi." |
|
4463 | 44 | 49 | ذق إنك أنت العزيز الكريم |
| | | (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!" |
|
4464 | 44 | 50 | إن هذا ما كنتم به تمترون |
| | | "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi." |
|