نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3468 | 30 | 59 | كذلك يطبع الله على قلوب الذين لا يعلمون |
| | | Kamar haka Allah Yake shãfe haske a kan zukãtan waɗanda ba su sani ba. |
|
3469 | 30 | 60 | فاصبر إن وعد الله حق ولا يستخفنك الذين لا يوقنون |
| | | Sabõda haka ka yi haƙuri lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma kada waɗanda bã su da yaƙĩni su sassabce maka hankali. |
|
3470 | 31 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم الم |
| | | A. L̃. M̃. |
|
3471 | 31 | 2 | تلك آيات الكتاب الحكيم |
| | | Waɗancan ãyõyin Littãfin ne mai hikima. |
|
3472 | 31 | 3 | هدى ورحمة للمحسنين |
| | | Shiriya da rahama ne ga mãsu kyautatawa. |
|
3473 | 31 | 4 | الذين يقيمون الصلاة ويؤتون الزكاة وهم بالآخرة هم يوقنون |
| | | Waɗanda ke tsai da salla kuma sunã ɓãyar da zakka kuma sũ, sunã yin ĩmãnin yaƙĩni, ga lãhira. |
|
3474 | 31 | 5 | أولئك على هدى من ربهم وأولئك هم المفلحون |
| | | Waɗannan sunã a kan shiriya ta daga Ubangijinsu kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. |
|
3475 | 31 | 6 | ومن الناس من يشتري لهو الحديث ليضل عن سبيل الله بغير علم ويتخذها هزوا أولئك لهم عذاب مهين |
| | | Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa. |
|
3476 | 31 | 7 | وإذا تتلى عليه آياتنا ولى مستكبرا كأن لم يسمعها كأن في أذنيه وقرا فبشره بعذاب أليم |
| | | Kuma idan an karanta ãyõyinMu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai, kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi. |
|
3477 | 31 | 8 | إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات لهم جنات النعيم |
| | | Lalle, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljannar ni'ima. |
|