نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
6095 | 94 | 5 | فإن مع العسر يسرا |
| | | To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. |
|
6096 | 94 | 6 | إن مع العسر يسرا |
| | | Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. |
|
6097 | 94 | 7 | فإذا فرغت فانصب |
| | | Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah). |
|
6098 | 94 | 8 | وإلى ربك فارغب |
| | | Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi. |
|
6099 | 95 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والتين والزيتون |
| | | Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn. |
|
6100 | 95 | 2 | وطور سينين |
| | | Da Dũr Sĩnĩna. |
|
6101 | 95 | 3 | وهذا البلد الأمين |
| | | Da wannan gari amintacce. |
|
6102 | 95 | 4 | لقد خلقنا الإنسان في أحسن تقويم |
| | | Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa. |
|
6103 | 95 | 5 | ثم رددناه أسفل سافلين |
| | | Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni |
|
6104 | 95 | 6 | إلا الذين آمنوا وعملوا الصالحات فلهم أجر غير ممنون |
| | | Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa. |
|