نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4765 | 52 | 30 | أم يقولون شاعر نتربص به ريب المنون |
| | | Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"? |
|
4766 | 52 | 31 | قل تربصوا فإني معكم من المتربصين |
| | | Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku." |
|
4767 | 52 | 32 | أم تأمرهم أحلامهم بهذا أم هم قوم طاغون |
| | | Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi? |
|
4768 | 52 | 33 | أم يقولون تقوله بل لا يؤمنون |
| | | Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba. |
|
4769 | 52 | 34 | فليأتوا بحديث مثله إن كانوا صادقين |
| | | Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne. |
|
4770 | 52 | 35 | أم خلقوا من غير شيء أم هم الخالقون |
| | | Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta? |
|
4771 | 52 | 36 | أم خلقوا السماوات والأرض بل لا يوقنون |
| | | Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba. |
|
4772 | 52 | 37 | أم عندهم خزائن ربك أم هم المصيطرون |
| | | Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya? |
|
4773 | 52 | 38 | أم لهم سلم يستمعون فيه فليأت مستمعهم بسلطان مبين |
| | | Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne. |
|
4774 | 52 | 39 | أم له البنات ولكم البنون |
| | | Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne? |
|