نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4538 | 46 | 28 | فلولا نصرهم الذين اتخذوا من دون الله قربانا آلهة بل ضلوا عنهم وذلك إفكهم وما كانوا يفترون |
| | | To, don mẽne ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abũbuwan yi. wa baiko, gumaka, ba su taimake su ba? Ã'a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa. |
|
4539 | 46 | 29 | وإذ صرفنا إليك نفرا من الجن يستمعون القرآن فلما حضروه قالوا أنصتوا فلما قضي ولوا إلى قومهم منذرين |
| | | Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi. |
|
4540 | 46 | 30 | قالوا يا قومنا إنا سمعنا كتابا أنزل من بعد موسى مصدقا لما بين يديه يهدي إلى الحق وإلى طريق مستقيم |
| | | Suka ce: "Ya mutãnenmu! Lalle mũ, mun ji wani littãfi an saukar da shi a bãyãn Mũsã, mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya. |
|
4541 | 46 | 31 | يا قومنا أجيبوا داعي الله وآمنوا به يغفر لكم من ذنوبكم ويجركم من عذاب أليم |
| | | "Yã mutãnenmu! Ku karɓa wa mai kiran Allah, kuma ku yi ĩmãni da Shi, Ya gãfarta muku daga zunubanku, kuma ya tserar da ku daga azãba mai raɗaɗi. |
|
4542 | 46 | 32 | ومن لا يجب داعي الله فليس بمعجز في الأرض وليس له من دونه أولياء أولئك في ضلال مبين |
| | | "Kuma wanda bai karɓa wa mai kiran Allah ba to bai zama mai buwãya a cikin ƙasa ba, kuma ba ya da waɗansu majiɓinta, baicin Shi. Waɗannnan sunã a cikin ɓata bayyananna." |
|
4543 | 46 | 33 | أولم يروا أن الله الذي خلق السماوات والأرض ولم يعي بخلقهن بقادر على أن يحيي الموتى بلى إنه على كل شيء قدير |
| | | Shin, kuma ba su gani ba cẽwa: "Lalle Allah, Wanda Yã halitta sammai da ƙasa kuma bai kãsa ga halittarsu ba, Mai ĩkon yi ne a kan rãyar da matattu?" Na'am, lalle Shi, Mai ĩkon yi ne a kan kõme. |
|
4544 | 46 | 34 | ويوم يعرض الذين كفروا على النار أليس هذا بالحق قالوا بلى وربنا قال فذوقوا العذاب بما كنتم تكفرون |
| | | Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, (a ce musu) "Ashe, wannan bã gaskiya ba ne?" Su ce: "Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!" Sai Ya ce, "To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci." |
|
4545 | 46 | 35 | فاصبر كما صبر أولو العزم من الرسل ولا تستعجل لهم كأنهم يوم يرون ما يوعدون لم يلبثوا إلا ساعة من نهار بلاغ فهل يهلك إلا القوم الفاسقون |
| | | Sabõda haka, ka yi haƙuri kamar yadda mãsu ƙarfin niyya daga Manzanni suka yi haƙuri. Kuma kada ka yi musu gaggãwa. Kamar dai sũ, a rãnar da suke ganin (sakamako) abin da ake yi musu wa'adi ba su zauna ba, fãce sa'a guda daga yini. Iyarwa dai da Manzanci). Shin, akwai wanda za a halakar? (Bãbu), fãce mutãne fasiƙai. |
|
4546 | 47 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم الذين كفروا وصدوا عن سبيل الله أضل أعمالهم |
| | | Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange mutãne daga tafarkin Allah, (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu. |
|
4547 | 47 | 2 | والذين آمنوا وعملوا الصالحات وآمنوا بما نزل على محمد وهو الحق من ربهم كفر عنهم سيئاتهم وأصلح بالهم |
| | | Kuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu. |
|