نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4337 | 43 | 12 | والذي خلق الأزواج كلها وجعل لكم من الفلك والأنعام ما تركبون |
| | | Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa. |
|
4338 | 43 | 13 | لتستووا على ظهوره ثم تذكروا نعمة ربكم إذا استويتم عليه وتقولوا سبحان الذي سخر لنا هذا وما كنا له مقرنين |
| | | Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba. |
|
4339 | 43 | 14 | وإنا إلى ربنا لمنقلبون |
| | | "Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu." |
|
4340 | 43 | 15 | وجعلوا له من عباده جزءا إن الإنسان لكفور مبين |
| | | Kuma suka sanya Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin. |
|
4341 | 43 | 16 | أم اتخذ مما يخلق بنات وأصفاكم بالبنين |
| | | Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza? |
|
4342 | 43 | 17 | وإذا بشر أحدهم بما ضرب للرحمن مثلا ظل وجهه مسودا وهو كظيم |
| | | Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki. |
|
4343 | 43 | 18 | أومن ينشأ في الحلية وهو في الخصام غير مبين |
| | | Ashe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba? |
|
4344 | 43 | 19 | وجعلوا الملائكة الذين هم عباد الرحمن إناثا أشهدوا خلقهم ستكتب شهادتهم ويسألون |
| | | Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su. |
|
4345 | 43 | 20 | وقالوا لو شاء الرحمن ما عبدناهم ما لهم بذلك من علم إن هم إلا يخرصون |
| | | Kuma suka ce: "Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba." Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi. |
|
4346 | 43 | 21 | أم آتيناهم كتابا من قبله فهم به مستمسكون |
| | | Kõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe? |
|