نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3977 | 38 | 7 | ما سمعنا بهذا في الملة الآخرة إن هذا إلا اختلاق |
| | | "Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya." |
|
3978 | 38 | 8 | أأنزل عليه الذكر من بيننا بل هم في شك من ذكري بل لما يذوقوا عذاب |
| | | "Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba. |
|
3979 | 38 | 9 | أم عندهم خزائن رحمة ربك العزيز الوهاب |
| | | Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta? |
|
3980 | 38 | 10 | أم لهم ملك السماوات والأرض وما بينهما فليرتقوا في الأسباب |
| | | Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu). |
|
3981 | 38 | 11 | جند ما هنالك مهزوم من الأحزاب |
| | | Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu. |
|
3982 | 38 | 12 | كذبت قبلهم قوم نوح وعاد وفرعون ذو الأوتاد |
| | | Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa). |
|
3983 | 38 | 13 | وثمود وقوم لوط وأصحاب الأيكة أولئك الأحزاب |
| | | Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, waɗancan ne ƙungiyõyin. |
|
3984 | 38 | 14 | إن كل إلا كذب الرسل فحق عقاب |
| | | Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba. |
|
3985 | 38 | 15 | وما ينظر هؤلاء إلا صيحة واحدة ما لها من فواق |
| | | Kuma waɗannan bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani. |
|
3986 | 38 | 16 | وقالوا ربنا عجل لنا قطنا قبل يوم الحساب |
| | | Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike." |
|