نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2622 | 22 | 27 | وأذن في الناس بالحج يأتوك رجالا وعلى كل ضامر يأتين من كل فج عميق |
| | | "Kuma ka yi yẽkuwa ga mutãne da wajabcin Hajji su je maka suna mãsu tafiya da ƙafãfu da kuma a kan kõwane maɗankwarin rãƙumi mãsu zuwa daga kõwane rango mai zurfi." |
|
2623 | 22 | 28 | ليشهدوا منافع لهم ويذكروا اسم الله في أيام معلومات على ما رزقهم من بهيمة الأنعام فكلوا منها وأطعموا البائس الفقير |
| | | "Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu sabõda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbõbin jin dãɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci." |
|
2624 | 22 | 29 | ثم ليقضوا تفثهم وليوفوا نذورهم وليطوفوا بالبيت العتيق |
| | | "Sa'an nan kuma sai su ƙãre ibãdarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawãfi (sunã gẽwaya) ga ¦ãkin nin 'yantacce." |
|
2625 | 22 | 30 | ذلك ومن يعظم حرمات الله فهو خير له عند ربه وأحلت لكم الأنعام إلا ما يتلى عليكم فاجتنبوا الرجس من الأوثان واجتنبوا قول الزور |
| | | Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbõbin ni'ima fãce abin da ake karantãwa a kanku. Sabõda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumãka kuma ku nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur. |
|
2626 | 22 | 31 | حنفاء لله غير مشركين به ومن يشرك بالله فكأنما خر من السماء فتخطفه الطير أو تهوي به الريح في مكان سحيق |
| | | Kuna mãsu tsayuwa ga gaskiya dõmin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yanã kamar abin da ya fãɗo daga sama, sa'an nan tsuntsãye su cafe shi, ko iska ta fãɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa. |
|
2627 | 22 | 32 | ذلك ومن يعظم شعائر الله فإنها من تقوى القلوب |
| | | Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita (girmamãwar) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda. |
|
2628 | 22 | 33 | لكم فيها منافع إلى أجل مسمى ثم محلها إلى البيت العتيق |
| | | Kuna da waɗansu abũbuwan amfãni a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattãta zuwa ga ¦ãkin 'yantacce ne. |
|
2629 | 22 | 34 | ولكل أمة جعلنا منسكا ليذكروا اسم الله على ما رزقهم من بهيمة الأنعام فإلهكم إله واحد فله أسلموا وبشر المخبتين |
| | | Kuma ga kõwace al'umma Mun sanya ibãdar yanka, dõmin su ambaci sũnan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbõbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushãra ga mãsu ƙanƙantar da kai. |
|
2630 | 22 | 35 | الذين إذا ذكر الله وجلت قلوبهم والصابرين على ما أصابهم والمقيمي الصلاة ومما رزقناهم ينفقون |
| | | Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukãtansu su firgita, da mãsu haƙuri a kan abin da ya sãme su, da mãsu tsayar da salla, kuma sunã ciyarwa daga abin da Muka azurta su. |
|
2631 | 22 | 36 | والبدن جعلناها لكم من شعائر الله لكم فيها خير فاذكروا اسم الله عليها صواف فإذا وجبت جنوبها فكلوا منها وأطعموا القانع والمعتر كذلك سخرناها لكم لعلكم تشكرون |
| | | Kuma rãƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibãdõjin Allah. Kunã da wani alhẽri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sunã tsaye a kan ƙafãfu uku. Sa'an nan idan sãsanninsu suka fãɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hõre muku su, tsammãninku kunã gõdẽwa. |
|