نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3917 | 37 | 129 | وتركنا عليه في الآخرين |
| | | Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe. |
|
3918 | 37 | 130 | سلام على إل ياسين |
| | | Aminci ya tabbata ga Ilyãs. |
|
3919 | 37 | 131 | إنا كذلك نجزي المحسنين |
| | | Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
|
3920 | 37 | 132 | إنه من عبادنا المؤمنين |
| | | Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. |
|
3921 | 37 | 133 | وإن لوطا لمن المرسلين |
| | | Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. |
|
3922 | 37 | 134 | إذ نجيناه وأهله أجمعين |
| | | A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya. |
|
3923 | 37 | 135 | إلا عجوزا في الغابرين |
| | | Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba). |
|
3924 | 37 | 136 | ثم دمرنا الآخرين |
| | | Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen. |
|
3925 | 37 | 137 | وإنكم لتمرون عليهم مصبحين |
| | | Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci. |
|
3926 | 37 | 138 | وبالليل أفلا تعقلون |
| | | Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba? |
|