نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3551 | 33 | 18 | قد يعلم الله المعوقين منكم والقائلين لإخوانهم هلم إلينا ولا يأتون البأس إلا قليلا |
| | | Lalle Allah Ya san mãsu hana mutãne fita daga cikinku, da mãsu cẽwa ga 'yan'uwansu,"Ku zo nan a wurinmu." Kuma bã zã su shiga yãƙi ba fãce kaɗan. |
|
3552 | 33 | 19 | أشحة عليكم فإذا جاء الخوف رأيتهم ينظرون إليك تدور أعينهم كالذي يغشى عليه من الموت فإذا ذهب الخوف سلقوكم بألسنة حداد أشحة على الخير أولئك لم يؤمنوا فأحبط الله أعمالهم وكان ذلك على الله يسيرا |
| | | Suna mãsu rõwa gare ku, sa'an nan idan tsõro ya zo, sai ka gan su sunã kallo zuwa gare ka, idãnunsu sunã kẽwaya, kamar wanda ake rufe hankalinsa sabõda mutuwa. Sa'an nan idan tsõron ya tafi, sai su yi muku miyãgun maganganu da harussa mãsu kaifi, sunã mãsu rõwa a kan dũkiya. Waɗannan, ba su yi ĩmani ba, sabõda hakaAllah Ya ɓãta ayyukansu. Kuma wannan ya kasance mai sauƙi ga Allah. |
|
3553 | 33 | 20 | يحسبون الأحزاب لم يذهبوا وإن يأت الأحزاب يودوا لو أنهم بادون في الأعراب يسألون عن أنبائكم ولو كانوا فيكم ما قاتلوا إلا قليلا |
| | | Sunã zaton ƙungiyõyin kãfirai ba su tafi ba. Kuma idan ƙungiyõyin kãfirai sun zo, sunã gũrin da dai sun zama a karkara a cikin ƙauyãwa, sunã tambayar lãbãranku. Kuma kõ dã sun kasance a cikinku, bã zã su yi yãƙi ba, fãce kaɗan. |
|
3554 | 33 | 21 | لقد كان لكم في رسول الله أسوة حسنة لمن كان يرجو الله واليوم الآخر وذكر الله كثيرا |
| | | Lalle, abin kõyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã fãtan rahamar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa. |
|
3555 | 33 | 22 | ولما رأى المؤمنون الأحزاب قالوا هذا ما وعدنا الله ورسوله وصدق الله ورسوله وما زادهم إلا إيمانا وتسليما |
| | | Kuma a lõkacin da mũminai suka ga ƙungiyõyin kãfirai, sai suka ce, "Wannan ne abin da Allah da ManzonSa suka yi mana wa'adi, Allah da ManzonSa sunyi gaskiya." Kuma wannan bai ƙãra musu kõme ba fãce ĩmãni da sallamãwa. |
|
3556 | 33 | 23 | من المؤمنين رجال صدقوا ما عاهدوا الله عليه فمنهم من قضى نحبه ومنهم من ينتظر وما بدلوا تبديلا |
| | | Daga mũminai akwai waɗansu mazãje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkwari a kansa, sa'an nan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukãtarsa, kuma daga cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa. |
|
3557 | 33 | 24 | ليجزي الله الصادقين بصدقهم ويعذب المنافقين إن شاء أو يتوب عليهم إن الله كان غفورا رحيما |
| | | Dõmin Allah Ya sãka wa masu gaskiya da gakiyarsu, kuma Ya azabtar da munafukai idan Ya so, ko Ya karɓi tũba a kansu. Lalle, Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. |
|
3558 | 33 | 25 | ورد الله الذين كفروا بغيظهم لم ينالوا خيرا وكفى الله المؤمنين القتال وكان الله قويا عزيزا |
| | | Kuma Allah Yã mayar da waɗanda suka kãfirta da fushinsu, ba su sãmi wani alhẽri ba. Allah Ya isar wa mũminai daga barin yãƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwãyi. |
|
3559 | 33 | 26 | وأنزل الذين ظاهروهم من أهل الكتاب من صياصيهم وقذف في قلوبهم الرعب فريقا تقتلون وتأسرون فريقا |
| | | Kuma Ya saukar da waɗannan da suka taimake su daga mazõwa Littãfi, daga birãnensu, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kunã kashẽwa, kuma kunã kãma wata ƙungiyar. |
|
3560 | 33 | 27 | وأورثكم أرضهم وديارهم وأموالهم وأرضا لم تطئوها وكان الله على كل شيء قديرا |
| | | Kuma Ya gãdar da ku gõnakinsu da gidãjensu da dũkiyõyinsu, da wata ƙasa wadda ba ku taɓa tãkarta bã. Kuma Allah ya kasance Mai ĩkon yi ne a kan kõme. |
|