نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3293 | 28 | 41 | وجعلناهم أئمة يدعون إلى النار ويوم القيامة لا ينصرون |
| | | Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta, kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba. |
|
3294 | 28 | 42 | وأتبعناهم في هذه الدنيا لعنة ويوم القيامة هم من المقبوحين |
| | | Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu. |
|
3295 | 28 | 43 | ولقد آتينا موسى الكتاب من بعد ما أهلكنا القرون الأولى بصائر للناس وهدى ورحمة لعلهم يتذكرون |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa. |
|
3296 | 28 | 44 | وما كنت بجانب الغربي إذ قضينا إلى موسى الأمر وما كنت من الشاهدين |
| | | Kuma ba ka kasance ba ga gẽfen rãfi na yamma a lõkacin da Muka hukunta al'amaru zuwa ga Mũsã, kuma ba ka kasance daga halartattu ba. |
|
3297 | 28 | 45 | ولكنا أنشأنا قرونا فتطاول عليهم العمر وما كنت ثاويا في أهل مدين تتلو عليهم آياتنا ولكنا كنا مرسلين |
| | | Kuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa (da kai game da waɗancan lãbarai). |
|
3298 | 28 | 46 | وما كنت بجانب الطور إذ نادينا ولكن رحمة من ربك لتنذر قوما ما أتاهم من نذير من قبلك لعلهم يتذكرون |
| | | Kuma ba ka kasance ga gẽfen dũtse ba a lõkacin da Muka yi kira, kuma amma dõmin rahama daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabãninka bai je musu ba, tsammãninsu sunã tunãwa. |
|
3299 | 28 | 47 | ولولا أن تصيبهم مصيبة بما قدمت أيديهم فيقولوا ربنا لولا أرسلت إلينا رسولا فنتبع آياتك ونكون من المؤمنين |
| | | Kuma bã dõmin wata masĩfa ta sãme su ba sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, su ce: "Yã Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bĩn ãyõyinKa, kuma mu kasance daga mũminai?" |
|
3300 | 28 | 48 | فلما جاءهم الحق من عندنا قالوا لولا أوتي مثل ما أوتي موسى أولم يكفروا بما أوتي موسى من قبل قالوا سحران تظاهرا وقالوا إنا بكل كافرون |
| | | Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga wurinMu, suka ce: "Don me ba a bã shi kamar abin da aka bai wa Mũsã ba?" Shin kuma ba su kãfirta ba da abin da aka bai wa Mũsã a gabãnin (wannan)? suka ce: "Sihirõri biyu ne suka taimaki jũna," kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mãsu kãfirta ne ga dukansu?" |
|
3301 | 28 | 49 | قل فأتوا بكتاب من عند الله هو أهدى منهما أتبعه إن كنتم صادقين |
| | | Ka ce: "To ku zo da wani littãfi daga, wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bĩ shi, idan kunkasance mãsu gaskiya." |
|
3302 | 28 | 50 | فإن لم يستجيبوا لك فاعلم أنما يتبعون أهواءهم ومن أضل ممن اتبع هواه بغير هدى من الله إن الله لا يهدي القوم الظالمين |
| | | To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai. |
|