نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3057 | 26 | 125 | إني لكم رسول أمين |
| | | "Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce." |
|
3058 | 26 | 126 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3059 | 26 | 127 | وما أسألكم عليه من أجر إن أجري إلا على رب العالمين |
| | | "Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu." |
|
3060 | 26 | 128 | أتبنون بكل ريع آية تعبثون |
| | | "Shin, kunã yin ginin sitadiyo a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?" |
|
3061 | 26 | 129 | وتتخذون مصانع لعلكم تخلدون |
| | | "Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?" |
|
3062 | 26 | 130 | وإذا بطشتم بطشتم جبارين |
| | | "Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa." |
|
3063 | 26 | 131 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3064 | 26 | 132 | واتقوا الذي أمدكم بما تعلمون |
| | | "Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani." |
|
3065 | 26 | 133 | أمدكم بأنعام وبنين |
| | | "Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya." |
|
3066 | 26 | 134 | وجنات وعيون |
| | | "Da gõnaki da marẽmari." |
|