نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2769 | 23 | 96 | ادفع بالتي هي أحسن السيئة نحن أعلم بما يصفون |
| | | Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ neMafi sani game da abin da suke siffantãwa. |
|
2770 | 23 | 97 | وقل رب أعوذ بك من همزات الشياطين |
| | | Ka ce: "Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu." |
|
2771 | 23 | 98 | وأعوذ بك رب أن يحضرون |
| | | "Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni, " |
|
2772 | 23 | 99 | حتى إذا جاء أحدهم الموت قال رب ارجعون |
| | | Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: "Yã Ubangijina, Ku mayar da ni (dũniya)." |
|
2773 | 23 | 100 | لعلي أعمل صالحا فيما تركت كلا إنها كلمة هو قائلها ومن ورائهم برزخ إلى يوم يبعثون |
| | | "Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su. |
|
2774 | 23 | 101 | فإذا نفخ في الصور فلا أنساب بينهم يومئذ ولا يتساءلون |
| | | Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba. |
|
2775 | 23 | 102 | فمن ثقلت موازينه فأولئك هم المفلحون |
| | | To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. |
|
2776 | 23 | 103 | ومن خفت موازينه فأولئك الذين خسروا أنفسهم في جهنم خالدون |
| | | Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama. |
|
2777 | 23 | 104 | تلفح وجوههم النار وهم فيها كالحون |
| | | Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne. |
|
2778 | 23 | 105 | ألم تكن آياتي تتلى عليكم فكنتم بها تكذبون |
| | | "Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa?" |
|