نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2551 | 21 | 68 | قالوا حرقوه وانصروا آلهتكم إن كنتم فاعلين |
| | | Suka ce: "Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa." |
|
2552 | 21 | 69 | قلنا يا نار كوني بردا وسلاما على إبراهيم |
| | | Muka ce: "Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm." |
|
2553 | 21 | 70 | وأرادوا به كيدا فجعلناهم الأخسرين |
| | | Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra. |
|
2554 | 21 | 71 | ونجيناه ولوطا إلى الأرض التي باركنا فيها للعالمين |
| | | Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai. |
|
2555 | 21 | 72 | ووهبنا له إسحاق ويعقوب نافلة وكلا جعلنا صالحين |
| | | Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai. |
|
2556 | 21 | 73 | وجعلناهم أئمة يهدون بأمرنا وأوحينا إليهم فعل الخيرات وإقام الصلاة وإيتاء الزكاة وكانوا لنا عابدين |
| | | Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu. |
|
2557 | 21 | 74 | ولوطا آتيناه حكما وعلما ونجيناه من القرية التي كانت تعمل الخبائث إنهم كانوا قوم سوء فاسقين |
| | | Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai. |
|
2558 | 21 | 75 | وأدخلناه في رحمتنا إنه من الصالحين |
| | | Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai. |
|
2559 | 21 | 76 | ونوحا إذ نادى من قبل فاستجبنا له فنجيناه وأهله من الكرب العظيم |
| | | Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma. |
|
2560 | 21 | 77 | ونصرناه من القوم الذين كذبوا بآياتنا إنهم كانوا قوم سوء فأغرقناهم أجمعين |
| | | Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya. |
|