نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2315 | 19 | 65 | رب السماوات والأرض وما بينهما فاعبده واصطبر لعبادته هل تعلم له سميا |
| | | Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautarsa. Shin kã san wani takwara a gare shi? |
|
2316 | 19 | 66 | ويقول الإنسان أإذا ما مت لسوف أخرج حيا |
| | | Kuma mutum yana cẽwa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai?" |
|
2317 | 19 | 67 | أولا يذكر الإنسان أنا خلقناه من قبل ولم يك شيئا |
| | | Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba? |
|
2318 | 19 | 68 | فوربك لنحشرنهم والشياطين ثم لنحضرنهم حول جهنم جثيا |
| | | To, Munã rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne. |
|
2319 | 19 | 69 | ثم لننزعن من كل شيعة أيهم أشد على الرحمن عتيا |
| | | Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya. |
|
2320 | 19 | 70 | ثم لنحن أعلم بالذين هم أولى بها صليا |
| | | Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗanda suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita. |
|
2321 | 19 | 71 | وإن منكم إلا واردها كان على ربك حتما مقضيا |
| | | Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata. Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce. |
|
2322 | 19 | 72 | ثم ننجي الذين اتقوا ونذر الظالمين فيها جثيا |
| | | Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne. |
|
2323 | 19 | 73 | وإذا تتلى عليهم آياتنا بينات قال الذين كفروا للذين آمنوا أي الفريقين خير مقاما وأحسن نديا |
| | | Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa?" |
|
2324 | 19 | 74 | وكم أهلكنا قبلهم من قرن هم أحسن أثاثا ورئيا |
| | | Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã. |
|