نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2154 | 18 | 14 | وربطنا على قلوبهم إذ قاموا فقالوا ربنا رب السماوات والأرض لن ندعو من دونه إلها لقد قلنا إذا شططا |
| | | Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: "Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi waninSa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare haddi a sa'an nan." |
|
2155 | 18 | 15 | هؤلاء قومنا اتخذوا من دونه آلهة لولا يأتون عليهم بسلطان بين فمن أظلم ممن افترى على الله كذبا |
| | | "Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar)? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah?" |
|
2156 | 18 | 16 | وإذ اعتزلتموهم وما يعبدون إلا الله فأووا إلى الكهف ينشر لكم ربكم من رحمته ويهيئ لكم من أمركم مرفقا |
| | | "Kuma idan kun nĩsance su sũ da abin da suke bautãwa, fãce Allah, to, ku tattara zuwa ga kõgon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamarSa kuma Ya sauƙaƙe muku madõgara daga al'amarinku." |
|
2157 | 18 | 17 | وترى الشمس إذا طلعت تزاور عن كهفهم ذات اليمين وإذا غربت تقرضهم ذات الشمال وهم في فجوة منه ذلك من آيات الله من يهد الله فهو المهتد ومن يضلل فلن تجد له وليا مرشدا |
| | | Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare shi. Wannan abu yanã daga ãyõyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shĩ ne mai shiryuwa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmar masa wani majiɓinci mai shiryarwa ba. |
|
2158 | 18 | 18 | وتحسبهم أيقاظا وهم رقود ونقلبهم ذات اليمين وذات الشمال وكلبهم باسط ذراعيه بالوصيد لو اطلعت عليهم لوليت منهم فرارا ولملئت منهم رعبا |
| | | Kuma kanã zaton su farkakku ne, alhãli kuwa sũ mãsu barci ne. Munã jũya su wajen dãma da wajen hagu, kuma karensu yanã shimfiɗe da zirã'õ'in ƙafãfuwansa ga farfãjiya (ta kõgon). Dã ka lẽka (a kan) su (dã) lalle ne, ka jũya daga gare su a guje kuma (dã) lalle ne ka cika da tsõro daga gare su. |
|
2159 | 18 | 19 | وكذلك بعثناهم ليتساءلوا بينهم قال قائل منهم كم لبثتم قالوا لبثنا يوما أو بعض يوم قالوا ربكم أعلم بما لبثتم فابعثوا أحدكم بورقكم هذه إلى المدينة فلينظر أيها أزكى طعاما فليأتكم برزق منه وليتلطف ولا يشعرن بكم أحدا |
| | | Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin. Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum." |
|
2160 | 18 | 20 | إنهم إن يظهروا عليكم يرجموكم أو يعيدوكم في ملتهم ولن تفلحوا إذا أبدا |
| | | "Lalle ne sũ idan sun kãmã ku, zã su jẽfẽ ku, kõ kuwa su mayar da ku a cikin addininsu kuma bã zã ku sãmi babban rabo, ba, a sa'an nan har abada." |
|
2161 | 18 | 21 | وكذلك أعثرنا عليهم ليعلموا أن وعد الله حق وأن الساعة لا ريب فيها إذ يتنازعون بينهم أمرهم فقالوا ابنوا عليهم بنيانا ربهم أعلم بهم قال الذين غلبوا على أمرهم لنتخذن عليهم مسجدا |
| | | Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su (gare su) dõmin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar al'amarinsu a tsakãninsu sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su." Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu riƙi masãllãci a kansu." |
|
2162 | 18 | 22 | سيقولون ثلاثة رابعهم كلبهم ويقولون خمسة سادسهم كلبهم رجما بالغيب ويقولون سبعة وثامنهم كلبهم قل ربي أعلم بعدتهم ما يعلمهم إلا قليل فلا تمار فيهم إلا مراء ظاهرا ولا تستفت فيهم منهم أحدا |
| | | Zã su ce: "Uku ne da na huɗunsu karensu."Kuma sunã cẽwa, "Biyar ne da na shidansu karensu," a kan jĩfa a cikin duhu. Kuma sunã cẽwa, "Bakwaine da na takwas ɗinsu karensu."Ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi saniga ƙidãyarsu, bãbu wanda ya san su fãce kaɗan."Kada ka yi jãyayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa ga kõwa daga gare su a cikin al'amarinsu. |
|
2163 | 18 | 23 | ولا تقولن لشيء إني فاعل ذلك غدا |
| | | Kuma kada lalle ka ce ga wani abu, "Lalle ni, mai aikatãwa ne ga wancan a gõbe." |
|