نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1445 | 10 | 81 | فلما ألقوا قال موسى ما جئتم به السحر إن الله سيبطله إن الله لا يصلح عمل المفسدين |
| | | To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: "Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata. |
|
1446 | 10 | 82 | ويحق الله الحق بكلماته ولو كره المجرمون |
| | | "Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi." |
|
1447 | 10 | 83 | فما آمن لموسى إلا ذرية من قومه على خوف من فرعون وملئهم أن يفتنهم وإن فرعون لعال في الأرض وإنه لمن المسرفين |
| | | Sa'an nan bãbu wanda ya yi ĩmãni da Mũsa fãce zuriya daga mutãnensa, a kan tsõron kada Fir'auna da shũgabanninsu su fitinẽ su. Lalle, haƙĩƙa, Fir'auna marinjãyi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga mãsu ɓarna. |
|
1448 | 10 | 84 | وقال موسى يا قوم إن كنتم آمنتم بالله فعليه توكلوا إن كنتم مسلمين |
| | | Kuma Mũsã ya ce: "Yã kũ mutãnena! Idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah, to, a gare Shi sai ku dõgara, idan kun kasance Musulmi." |
|
1449 | 10 | 85 | فقالوا على الله توكلنا ربنا لا تجعلنا فتنة للقوم الظالمين |
| | | Sai suka ce: "Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu fitina ga mutãne azzãlumai. |
|
1450 | 10 | 86 | ونجنا برحمتك من القوم الكافرين |
| | | "Kuma Ka kuɓutar da mu dõmin RahamarKa, daga mutãne kãfirai." |
|
1451 | 10 | 87 | وأوحينا إلى موسى وأخيه أن تبوآ لقومكما بمصر بيوتا واجعلوا بيوتكم قبلة وأقيموا الصلاة وبشر المؤمنين |
| | | Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutãnenku a Masar a cikin wasu gidãje. Kuma ku sanya gidãjenku su fuskanci Alƙibla, kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bãyar da bushãra ga mãsu ĩmãni. |
|
1452 | 10 | 88 | وقال موسى ربنا إنك آتيت فرعون وملأه زينة وأموالا في الحياة الدنيا ربنا ليضلوا عن سبيلك ربنا اطمس على أموالهم واشدد على قلوبهم فلا يؤمنوا حتى يروا العذاب الأليم |
| | | Sai MũSã ya ce: "Yã Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyõyi a cikin rãyuwar dũniya, yã Ubangijinmu, dõmin su ɓatar (damutãne) daga hanyarKa. Yã Ubangijinmu! Ka shãfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri a kan zukãtansu yadda bã zã su yi ĩmãni ba har su ga azãba mai raɗaɗi." |
|
1453 | 10 | 89 | قال قد أجيبت دعوتكما فاستقيما ولا تتبعان سبيل الذين لا يعلمون |
| | | (Allah) Yã ce: "Lalle ne an karɓi addu'arku. Sai ku daidaitu kuma kada ku bi hanyar waɗanda ba su sani ba." |
|
1454 | 10 | 90 | وجاوزنا ببني إسرائيل البحر فأتبعهم فرعون وجنوده بغيا وعدوا حتى إذا أدركه الغرق قال آمنت أنه لا إله إلا الذي آمنت به بنو إسرائيل وأنا من المسلمين |
| | | Kuma Muka ƙẽtãrar da Banĩ Isrã'ila tẽku sai Fir'auna da rundunarsa suka bĩ su bisa ga zãlunci da ƙẽtare haddi, har a lõkacin da nutsẽwa ta riske shi ya ce: "Nã yi ĩmãni cẽwa, haƙĩƙa, bãbu abin bautawa fãce wannan da Banũ Isrã'il suka yi ĩmãni da Shi, kumanĩ, ina daga Musulmi." |
|