نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1414 | 10 | 50 | قل أرأيتم إن أتاكم عذابه بياتا أو نهارا ماذا يستعجل منه المجرمون |
| | | Ka ce: "Shin, kun gani, idan azãbarSa ta zo muku da dare ko da rãna? Mẽne ne daga gare shimãsu laifi suke nẽman gaggãwarsa?" |
|
1415 | 10 | 51 | أثم إذا ما وقع آمنتم به آلآن وقد كنتم به تستعجلون |
| | | Shin sa'an nan kuma idan har ya auku, kun yi ĩmãni da shi? Ashe? Yanzu kuwa, alhãli kun kasance game da shi kunã nẽman gaggãwar aukuwarsa? |
|
1416 | 10 | 52 | ثم قيل للذين ظلموا ذوقوا عذاب الخلد هل تجزون إلا بما كنتم تكسبون |
| | | Sa'an nan kuma aka ce ga waɗanda suka yi zãlunci, "Ku ɗanɗani azãbar dawwama! Shin, anã sãka muku fãce da abin da kuka kasance kuna aikatãwa?" |
|
1417 | 10 | 53 | ويستنبئونك أحق هو قل إي وربي إنه لحق وما أنتم بمعجزين |
| | | Kuma sunã tambayar ka: Shin gaskiya ne? Ka ce: "Ĩ, ina rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle gaskiya ne, kuma ba ku zama mãsu buwãya ba." |
|
1418 | 10 | 54 | ولو أن لكل نفس ظلمت ما في الأرض لافتدت به وأسروا الندامة لما رأوا العذاب وقضي بينهم بالقسط وهم لا يظلمون |
| | | Kuma dã kõwane rai wanda ya yi zãlunci yã mallaki duka abin da yake a cikin ƙasa, to, dã yã yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma bã zã a zãlunce su ba. |
|
1419 | 10 | 55 | ألا إن لله ما في السماوات والأرض ألا إن وعد الله حق ولكن أكثرهم لا يعلمون |
| | | To! Haƙĩƙa Allah Ya mallaki abin da yake a cikin sammai da ƙasa. To! Haƙĩƙa wa'adin Allah gaskiya ne. Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba. |
|
1420 | 10 | 56 | هو يحيي ويميت وإليه ترجعون |
| | | Shi ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma zuwa gare Shi ne ake mayar da ku. |
|
1421 | 10 | 57 | يا أيها الناس قد جاءتكم موعظة من ربكم وشفاء لما في الصدور وهدى ورحمة للمؤمنين |
| | | Ya ku mutãne! Lalle wa'azi yã jẽ muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙirãza, da shiriya da rahama ga muminai. |
|
1422 | 10 | 58 | قل بفضل الله وبرحمته فبذلك فليفرحوا هو خير مما يجمعون |
| | | Ka ce: "Da falalar Allah da rahamarSa. Sai su yi farin ciki da wannan." Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa. |
|
1423 | 10 | 59 | قل أرأيتم ما أنزل الله لكم من رزق فجعلتم منه حراما وحلالا قل آلله أذن لكم أم على الله تفترون |
| | | Ka ce: "Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar sabõda ku na arziki, sai kuka sanya hukuncin haramci da halacci a gare shi?" Ka ce: "Shin, Allah ne Ya yi muku izni, ko ga Allah kuke ƙirƙirãwar ƙarya?" |
|