نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1319 | 9 | 84 | ولا تصل على أحد منهم مات أبدا ولا تقم على قبره إنهم كفروا بالله ورسوله وماتوا وهم فاسقون |
| | | Kuma kada ka yi salla a kan kõwa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lalle ne sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma sun mutu alhãli kuwa sunã fãsiƙai. |
|
1320 | 9 | 85 | ولا تعجبك أموالهم وأولادهم إنما يريد الله أن يعذبهم بها في الدنيا وتزهق أنفسهم وهم كافرون |
| | | Kuma kada dũkiyõyinsu da ɗiyansu su bã ka sha'awa. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba da su a cikin dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai. |
|
1321 | 9 | 86 | وإذا أنزلت سورة أن آمنوا بالله وجاهدوا مع رسوله استأذنك أولو الطول منهم وقالوا ذرنا نكن مع القاعدين |
| | | Kuma idan aka saukar da wata sũra cẽwa; Ku yi ĩmãni da Allah kuma ku yi jihãdi tãre da ManzionSa. Sai mawadãta daga gare su su nẽmi izninka, kuma su ce: Ka bar mu mu kasance tãre da mazauna. |
|
1322 | 9 | 87 | رضوا بأن يكونوا مع الخوالف وطبع على قلوبهم فهم لا يفقهون |
| | | Sun yarda da su kasance tãre da mãtã mãsu zama (a cikin gidãje). Kuma aka rufe a kan zukãtansu, sabõda haka, sũ, bã su fahimta. |
|
1323 | 9 | 88 | لكن الرسول والذين آمنوا معه جاهدوا بأموالهم وأنفسهم وأولئك لهم الخيرات وأولئك هم المفلحون |
| | | Amma Manzon Allah da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sun yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu. Kuma waɗannan sunã da ayyukan alhẽri, kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara. |
|
1324 | 9 | 89 | أعد الله لهم جنات تجري من تحتها الأنهار خالدين فيها ذلك الفوز العظيم |
| | | Allah yã yi musu tattalin gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu. Wancan ne babban rabo mai girma. |
|
1325 | 9 | 90 | وجاء المعذرون من الأعراب ليؤذن لهم وقعد الذين كذبوا الله ورسوله سيصيب الذين كفروا منهم عذاب أليم |
| | | Kuma mãsu uzuri daga ƙauyãwa zuka zo dõmin a yi musu izini, kuma waɗanda suka yi wa Allah da ManzonSa ƙarya, suka yi zamansu. wata azãba mai raɗaɗi zã ta sãmi waɗanda suka kãfirta daga gare su. |
|
1326 | 9 | 91 | ليس على الضعفاء ولا على المرضى ولا على الذين لا يجدون ما ينفقون حرج إذا نصحوا لله ورسوله ما على المحسنين من سبيل والله غفور رحيم |
| | | Bãbu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma bãbu laifi a kan waɗanda bã su sãmun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasĩha ga Allah da ManzonSa. Kuma bãbu wani laifi a kan mãsu kyautatãwa. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai tausayi. |
|
1327 | 9 | 92 | ولا على الذين إذا ما أتوك لتحملهم قلت لا أجد ما أحملكم عليه تولوا وأعينهم تفيض من الدمع حزنا ألا يجدوا ما ينفقون |
| | | Kuma bãbu (laifi) a kan waɗanda idan sun je maka dõmin ka ɗauke su ka ce: "Bã ni da abin da nake ɗaukar ku a kansa," suka jũya alhãli kuwa idãnunsu sunã zubar da hawãye dõmin baƙin ciki cẽwa ba su sãmi abin da suke ciyarwa ba. |
|
1328 | 9 | 93 | إنما السبيل على الذين يستأذنونك وهم أغنياء رضوا بأن يكونوا مع الخوالف وطبع الله على قلوبهم فهم لا يعلمون |
| | | Abin sani kawai, laifi Yanã a kan waɗanda suke nẽman izininka alhãli kuwa sũ mawadãta ne. Sun yarda su kasance tãre da mãtã mamaya (gidãje), kuma Allah Yã danne a kan zukãtansu, dõmin haka sũ, bã su gãnẽwa. |
|