نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
5586 | 75 | 35 | ثم أولى لك فأولى |
| | | Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa. |
|
5587 | 75 | 36 | أيحسب الإنسان أن يترك سدى |
| | | Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)? |
|
5588 | 75 | 37 | ألم يك نطفة من مني يمنى |
| | | Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa) |
|
5589 | 75 | 38 | ثم كان علقة فخلق فسوى |
| | | Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa; |
|
5590 | 75 | 39 | فجعل منه الزوجين الذكر والأنثى |
| | | Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace? |
|
5591 | 75 | 40 | أليس ذلك بقادر على أن يحيي الموتى |
| | | Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu? |
|
5592 | 76 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم هل أتى على الإنسان حين من الدهر لم يكن شيئا مذكورا |
| | | Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata. |
|
5593 | 76 | 2 | إنا خلقنا الإنسان من نطفة أمشاج نبتليه فجعلناه سميعا بصيرا |
| | | Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani, |
|
5594 | 76 | 3 | إنا هديناه السبيل إما شاكرا وإما كفورا |
| | | Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci. |
|
5595 | 76 | 4 | إنا أعتدنا للكافرين سلاسل وأغلالا وسعيرا |
| | | Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr. |
|