نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3627 | 34 | 21 | وما كان له عليهم من سلطان إلا لنعلم من يؤمن بالآخرة ممن هو منها في شك وربك على كل شيء حفيظ |
| | | Kuma bã ya da wani dalĩli a kansu fãce dai dõmin Mu san wanda yake yin ĩmãni da Lãhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kõme, Mai tsaro ne. |
|
3628 | 34 | 22 | قل ادعوا الذين زعمتم من دون الله لا يملكون مثقال ذرة في السماوات ولا في الأرض وما لهم فيهما من شرك وما له منهم من ظهير |
| | | Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa), kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su. |
|
3629 | 34 | 23 | ولا تنفع الشفاعة عنده إلا لمن أذن له حتى إذا فزع عن قلوبهم قالوا ماذا قال ربكم قالوا الحق وهو العلي الكبير |
| | | "Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurinSa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma," |
|
3630 | 34 | 24 | قل من يرزقكم من السماوات والأرض قل الله وإنا أو إياكم لعلى هدى أو في ضلال مبين |
| | | Ka ce: "Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?" Ka ce: "Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya." |
|
3631 | 34 | 25 | قل لا تسألون عما أجرمنا ولا نسأل عما تعملون |
| | | Ka ce: "Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba." |
|
3632 | 34 | 26 | قل يجمع بيننا ربنا ثم يفتح بيننا بالحق وهو الفتاح العليم |
| | | Ka ce: "Ubangijinmu zai tãra tsakãninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani." |
|
3633 | 34 | 27 | قل أروني الذين ألحقتم به شركاء كلا بل هو الله العزيز الحكيم |
| | | Ka ce: "Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima." |
|
3634 | 34 | 28 | وما أرسلناك إلا كافة للناس بشيرا ونذيرا ولكن أكثر الناس لا يعلمون |
| | | Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. |
|
3635 | 34 | 29 | ويقولون متى هذا الوعد إن كنتم صادقين |
| | | Sunã cẽwa, "Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance mãsu gaskiya?" |
|
3636 | 34 | 30 | قل لكم ميعاد يوم لا تستأخرون عنه ساعة ولا تستقدمون |
| | | Ka ce: "Kunã da mi'ãdin wani yini wanda bã ku jinkirta daga gare shi kõ da sa'a ɗaya, kuma bã ku gabãta." |
|