نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3558 | 33 | 25 | ورد الله الذين كفروا بغيظهم لم ينالوا خيرا وكفى الله المؤمنين القتال وكان الله قويا عزيزا |
| | | Kuma Allah Yã mayar da waɗanda suka kãfirta da fushinsu, ba su sãmi wani alhẽri ba. Allah Ya isar wa mũminai daga barin yãƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwãyi. |
|
3559 | 33 | 26 | وأنزل الذين ظاهروهم من أهل الكتاب من صياصيهم وقذف في قلوبهم الرعب فريقا تقتلون وتأسرون فريقا |
| | | Kuma Ya saukar da waɗannan da suka taimake su daga mazõwa Littãfi, daga birãnensu, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kunã kashẽwa, kuma kunã kãma wata ƙungiyar. |
|
3560 | 33 | 27 | وأورثكم أرضهم وديارهم وأموالهم وأرضا لم تطئوها وكان الله على كل شيء قديرا |
| | | Kuma Ya gãdar da ku gõnakinsu da gidãjensu da dũkiyõyinsu, da wata ƙasa wadda ba ku taɓa tãkarta bã. Kuma Allah ya kasance Mai ĩkon yi ne a kan kõme. |
|
3561 | 33 | 28 | يا أيها النبي قل لأزواجك إن كنتن تردن الحياة الدنيا وزينتها فتعالين أمتعكن وأسرحكن سراحا جميلا |
| | | Yã kai Annabi! Ka ce wa matanka, "Idan kun kasance kunã nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, to, ku zo in yi muku kyautar ban kwãna kuma in sake ku, saki mai kyau." |
|
3562 | 33 | 29 | وإن كنتن تردن الله ورسوله والدار الآخرة فإن الله أعد للمحسنات منكن أجرا عظيما |
| | | "Kuma idan kun kasance kunã nufin Allah da Manzonsa da gidan Lãhria, to, lalle, Allah Yã yi tattalin wani sakamako mai girma ga mãsu kyautatãwa daga gare ku." |
|
3563 | 33 | 30 | يا نساء النبي من يأت منكن بفاحشة مبينة يضاعف لها العذاب ضعفين وكان ذلك على الله يسيرا |
| | | Yã mãtan Annabi! Wadda ta zo da alfãsha bayyananna daga cikinku zã a ninka mata azãba ninki biyu. Kuma wancan yã kasance mai sauƙi ga Allah. |
|
3564 | 33 | 31 | ومن يقنت منكن لله ورسوله وتعمل صالحا نؤتها أجرها مرتين وأعتدنا لها رزقا كريما |
| | | Kuma wadda ta yi tawãli'u daga cikinku ga Allah da ManzonSa, kuma ta aikata aiki na ƙwarai, zã Mu bã ta sakamakonta ninki biyu, kuma Mun yi mata tattalin arziki ma karimci. |
|
3565 | 33 | 32 | يا نساء النبي لستن كأحد من النساء إن اتقيتن فلا تخضعن بالقول فيطمع الذي في قلبه مرض وقلن قولا معروفا |
| | | Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kun yi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri. |
|
3566 | 33 | 33 | وقرن في بيوتكن ولا تبرجن تبرج الجاهلية الأولى وأقمن الصلاة وآتين الزكاة وأطعن الله ورسوله إنما يريد الله ليذهب عنكم الرجس أهل البيت ويطهركم تطهيرا |
| | | Kuma ku tabbata a cikin gidãjenku, kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar gãye-gãye ta jãhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩ da salla, kuma ku bãyar da zakka, ku yi ɗã, ã ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa. |
|
3567 | 33 | 34 | واذكرن ما يتلى في بيوتكن من آيات الله والحكمة إن الله كان لطيفا خبيرا |
| | | Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin ɗãkunanku daga ãyõyin Allah da hukunci. Lalle Allah Yã kasance Mai tausasãwa Mai labartawa. |
|