نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3408 | 29 | 68 | ومن أظلم ممن افترى على الله كذبا أو كذب بالحق لما جاءه أليس في جهنم مثوى للكافرين |
| | | Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, kõ kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama bãbu mazauna ga kãfirai? |
|
3409 | 29 | 69 | والذين جاهدوا فينا لنهدينهم سبلنا وإن الله لمع المحسنين |
| | | Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa (ga addĩninsu). |
|
3410 | 30 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم الم |
| | | A. L̃. M̃. |
|
3411 | 30 | 2 | غلبت الروم |
| | | An rinjãyi Rũmawa. |
|
3412 | 30 | 3 | في أدنى الأرض وهم من بعد غلبهم سيغلبون |
| | | A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya. |
|
3413 | 30 | 4 | في بضع سنين لله الأمر من قبل ومن بعد ويومئذ يفرح المؤمنون |
| | | A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki. |
|
3414 | 30 | 5 | بنصر الله ينصر من يشاء وهو العزيز الرحيم |
| | | Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. |
|
3415 | 30 | 6 | وعد الله لا يخلف الله وعده ولكن أكثر الناس لا يعلمون |
| | | Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. |
|
3416 | 30 | 7 | يعلمون ظاهرا من الحياة الدنيا وهم عن الآخرة هم غافلون |
| | | Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar Lãhira. |
|
3417 | 30 | 8 | أولم يتفكروا في أنفسهم ما خلق الله السماوات والأرض وما بينهما إلا بالحق وأجل مسمى وإن كثيرا من الناس بلقاء ربهم لكافرون |
| | | Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu? |
|