نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3108 | 26 | 176 | كذب أصحاب الأيكة المرسلين |
| | | Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni. |
|
3109 | 26 | 177 | إذ قال لهم شعيب ألا تتقون |
| | | A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" |
|
3110 | 26 | 178 | إني لكم رسول أمين |
| | | "Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce." |
|
3111 | 26 | 179 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3112 | 26 | 180 | وما أسألكم عليه من أجر إن أجري إلا على رب العالمين |
| | | "Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." |
|
3113 | 26 | 181 | أوفوا الكيل ولا تكونوا من المخسرين |
| | | "Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)." |
|
3114 | 26 | 182 | وزنوا بالقسطاس المستقيم |
| | | "Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce." |
|
3115 | 26 | 183 | ولا تبخسوا الناس أشياءهم ولا تعثوا في الأرض مفسدين |
| | | "Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna." |
|
3116 | 26 | 184 | واتقوا الذي خلقكم والجبلة الأولين |
| | | "Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko." |
|
3117 | 26 | 185 | قالوا إنما أنت من المسحرين |
| | | Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne." |
|