نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3088 | 26 | 156 | ولا تمسوها بسوء فيأخذكم عذاب يوم عظيم |
| | | "Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku." |
|
3089 | 26 | 157 | فعقروها فأصبحوا نادمين |
| | | Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma. |
|
3090 | 26 | 158 | فأخذهم العذاب إن في ذلك لآية وما كان أكثرهم مؤمنين |
| | | Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba. |
|
3091 | 26 | 159 | وإن ربك لهو العزيز الرحيم |
| | | Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai. |
|
3092 | 26 | 160 | كذبت قوم لوط المرسلين |
| | | Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni. |
|
3093 | 26 | 161 | إذ قال لهم أخوهم لوط ألا تتقون |
| | | A lõkacin da ɗan'uwansu, Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" |
|
3094 | 26 | 162 | إني لكم رسول أمين |
| | | "Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce." |
|
3095 | 26 | 163 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3096 | 26 | 164 | وما أسألكم عليه من أجر إن أجري إلا على رب العالمين |
| | | "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." |
|
3097 | 26 | 165 | أتأتون الذكران من العالمين |
| | | "Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?" |
|