نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3038 | 26 | 106 | إذ قال لهم أخوهم نوح ألا تتقون |
| | | A lõkacin da ɗan'uwansu, Nũhu, ya ce musu, "Shin, bã zã ku yi taƙawa ba?" |
|
3039 | 26 | 107 | إني لكم رسول أمين |
| | | "Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce." |
|
3040 | 26 | 108 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3041 | 26 | 109 | وما أسألكم عليه من أجر إن أجري إلا على رب العالمين |
| | | "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." |
|
3042 | 26 | 110 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3043 | 26 | 111 | قالوا أنؤمن لك واتبعك الأرذلون |
| | | Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?" |
|
3044 | 26 | 112 | قال وما علمي بما كانوا يعملون |
| | | Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa." |
|
3045 | 26 | 113 | إن حسابهم إلا على ربي لو تشعرون |
| | | "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa." |
|
3046 | 26 | 114 | وما أنا بطارد المؤمنين |
| | | "Ban zama mai kõre mũminai ba." |
|
3047 | 26 | 115 | إن أنا إلا نذير مبين |
| | | "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa." |
|