نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3028 | 26 | 96 | قالوا وهم فيها يختصمون |
| | | Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma, |
|
3029 | 26 | 97 | تالله إن كنا لفي ضلال مبين |
| | | "Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna." |
|
3030 | 26 | 98 | إذ نسويكم برب العالمين |
| | | "A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu. |
|
3031 | 26 | 99 | وما أضلنا إلا المجرمون |
| | | "Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi." |
|
3032 | 26 | 100 | فما لنا من شافعين |
| | | "Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta." |
|
3033 | 26 | 101 | ولا صديق حميم |
| | | "Kuma bã mu da abõki, masõyi." |
|
3034 | 26 | 102 | فلو أن لنا كرة فنكون من المؤمنين |
| | | "Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!" |
|
3035 | 26 | 103 | إن في ذلك لآية وما كان أكثرهم مؤمنين |
| | | Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba. |
|
3036 | 26 | 104 | وإن ربك لهو العزيز الرحيم |
| | | Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. |
|
3037 | 26 | 105 | كذبت قوم نوح المرسلين |
| | | Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni. |
|