نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2992 | 26 | 60 | فأتبعوهم مشرقين |
| | | Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã. |
|
2993 | 26 | 61 | فلما تراءى الجمعان قال أصحاب موسى إنا لمدركون |
| | | Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne." |
|
2994 | 26 | 62 | قال كلا إن معي ربي سيهدين |
| | | Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni." |
|
2995 | 26 | 63 | فأوحينا إلى موسى أن اضرب بعصاك البحر فانفلق فكان كل فرق كالطود العظيم |
| | | Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma. |
|
2996 | 26 | 64 | وأزلفنا ثم الآخرين |
| | | Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can. |
|
2997 | 26 | 65 | وأنجينا موسى ومن معه أجمعين |
| | | Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya. |
|
2998 | 26 | 66 | ثم أغرقنا الآخرين |
| | | Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen. |
|
2999 | 26 | 67 | إن في ذلك لآية وما كان أكثرهم مؤمنين |
| | | Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba. |
|
3000 | 26 | 68 | وإن ربك لهو العزيز الرحيم |
| | | Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai. |
|
3001 | 26 | 69 | واتل عليهم نبأ إبراهيم |
| | | Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm. |
|