نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2399 | 20 | 51 | قال فما بال القرون الأولى |
| | | Ya ce: "To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko?" |
|
2400 | 20 | 52 | قال علمها عند ربي في كتاب لا يضل ربي ولا ينسى |
| | | Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa." |
|
2401 | 20 | 53 | الذي جعل لكم الأرض مهدا وسلك لكم فيها سبلا وأنزل من السماء ماء فأخرجنا به أزواجا من نبات شتى |
| | | "Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam. |
|
2402 | 20 | 54 | كلوا وارعوا أنعامكم إن في ذلك لآيات لأولي النهى |
| | | Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali. |
|
2403 | 20 | 55 | منها خلقناكم وفيها نعيدكم ومنها نخرجكم تارة أخرى |
| | | Daga gare ta Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam. |
|
2404 | 20 | 56 | ولقد أريناه آياتنا كلها فكذب وأبى |
| | | Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyinMu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya! |
|
2405 | 20 | 57 | قال أجئتنا لتخرجنا من أرضنا بسحرك يا موسى |
| | | Ya ce: "Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã?" |
|
2406 | 20 | 58 | فلنأتينك بسحر مثله فاجعل بيننا وبينك موعدا لا نخلفه نحن ولا أنت مكانا سوى |
| | | "To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa." |
|
2407 | 20 | 59 | قال موعدكم يوم الزينة وأن يحشر الناس ضحى |
| | | Ya ce: "Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi." |
|
2408 | 20 | 60 | فتولى فرعون فجمع كيده ثم أتى |
| | | Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo. |
|