نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1742 | 13 | 35 | مثل الجنة التي وعد المتقون تجري من تحتها الأنهار أكلها دائم وظلها تلك عقبى الذين اتقوا وعقبى الكافرين النار |
| | | Misãlin Aljanna wadda aka yi alkawarinta ga mãsu taƙawa, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinta. Abincinta yana madawwami da inuwarta. Waccan ce ãƙibar waɗanda suka yi taƙawa, kuma ãƙibar kãfirai, ita ce wuta, |
|
1743 | 13 | 36 | والذين آتيناهم الكتاب يفرحون بما أنزل إليك ومن الأحزاب من ينكر بعضه قل إنما أمرت أن أعبد الله ولا أشرك به إليه أدعو وإليه مآب |
| | | Kuma waɗanda Muka bã su Littãfi sunã farin ciki da abin da aka saukar zuwa gare ka, kuma daga ƙungiyõyi akwai mai musun sãshensa. Ka ce: "Abin sani kawai, an umurce ni da in bauta wa Allah kuma kada in yi shirka da Shi, zuwa gare Shi nake kira, kuma zuwa gare Shi makõmata take." |
|
1744 | 13 | 37 | وكذلك أنزلناه حكما عربيا ولئن اتبعت أهواءهم بعدما جاءك من العلم ما لك من الله من ولي ولا واق |
| | | Kuma kamar wancan ne Muka saukar da shi, Hukunci a cikin Lãrabci. Kuma lalle ne idan kã bi son zuciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bãbu wani masõyi a gare ka mai kãre ka daga Allah, kuma bãbu matsari. |
|
1745 | 13 | 38 | ولقد أرسلنا رسلا من قبلك وجعلنا لهم أزواجا وذرية وما كان لرسول أن يأتي بآية إلا بإذن الله لكل أجل كتاب |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabãninka, kuma Muka sanya mãtan aure a gare su da zũriyya, kuma ba ya kasancẽwa ga wani Manzo ya zo da wata ãyã, sai da iznin Allah. Ga kõwane ajali akwai littãfi. |
|
1746 | 13 | 39 | يمحو الله ما يشاء ويثبت وعنده أم الكتاب |
| | | Allah Yanã shafe abin da Yake so, kuma Yanã tabbatarwa kuma a wurinsa asalin Littãfin yake. |
|
1747 | 13 | 40 | وإن ما نرينك بعض الذي نعدهم أو نتوفينك فإنما عليك البلاغ وعلينا الحساب |
| | | Kuma imma lalle Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu wa'adi, kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka to abin sani kawai iyarwa ce a kanka, kuma hisãbi yana gare Mu. |
|
1748 | 13 | 41 | أولم يروا أنا نأتي الأرض ننقصها من أطرافها والله يحكم لا معقب لحكمه وهو سريع الحساب |
| | | Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne, Muna jẽ wa ƙasar (su), Munã rage ta daga gẽfunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shĩ ne Mai gaggãwar sakamako. |
|
1749 | 13 | 42 | وقد مكر الذين من قبلهم فلله المكر جميعا يعلم ما تكسب كل نفس وسيعلم الكفار لمن عقبى الدار |
| | | Kuma lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci. To, ga Allah mãkircin yake gabã ɗaya. Ya san abin da kõwane rai yake tãnada. Kuma kãfirai zã su sani, ga wane ãƙibar gida take. |
|
1750 | 13 | 43 | ويقول الذين كفروا لست مرسلا قل كفى بالله شهيدا بيني وبينكم ومن عنده علم الكتاب |
| | | Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Ba a aiko ka ba." Ka ce, "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da tsakãninku da wanda yake a wurinsa akwai ilmin Littãfi." |
|
1751 | 14 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم الر كتاب أنزلناه إليك لتخرج الناس من الظلمات إلى النور بإذن ربهم إلى صراط العزيز الحميد |
| | | A. L̃.R. Littãfi ne mun saukar da shi zuwa gare ka dõmin ka fitar da mutãne daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin Mabuwãyi, Abin gõdẽwa. |
|