نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1560 | 11 | 87 | قالوا يا شعيب أصلاتك تأمرك أن نترك ما يعبد آباؤنا أو أن نفعل في أموالنا ما نشاء إنك لأنت الحليم الرشيد |
| | | Suka ce: "Yã Shu'aibu! Shin sallarka ce take umurtar ka ga mu bar abin da ubanninmu suke bautãwa, kõ kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin dũkiyõyinmu? Lalle, haƙĩƙa kai ne mai haƙuri shiryayye!" |
|
1561 | 11 | 88 | قال يا قوم أرأيتم إن كنت على بينة من ربي ورزقني منه رزقا حسنا وما أريد أن أخالفكم إلى ما أنهاكم عنه إن أريد إلا الإصلاح ما استطعت وما توفيقي إلا بالله عليه توكلت وإليه أنيب |
| | | Ya ce: "Ya mutãnena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyãwo daga gare Shi? Kuma bã ni nufin in sãɓa muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bã ni nufin kõme fãce gyãrã, gwargwadon da na sãmi dãma. Kuma muwãfaƙãta ba ta zama ba fãce daga Allah. A gare shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala." |
|
1562 | 11 | 89 | ويا قوم لا يجرمنكم شقاقي أن يصيبكم مثل ما أصاب قوم نوح أو قوم هود أو قوم صالح وما قوم لوط منكم ببعيد |
| | | "Kuma ya mutãnena! Kada sãɓa mini ya ɗauke ku ga misãlin abin da ya sãmi mutãnen Nũhu kõ kuwa mutãnen Hũdu kõ kuwa mutãnen Sãlihu ya sãme ku. Mutãnen Lũɗu ba su zama a wuri mai nĩsa ba daga gare ku." |
|
1563 | 11 | 90 | واستغفروا ربكم ثم توبوا إليه إن ربي رحيم ودود |
| | | "Kuma ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare shi. Lalle Ubangijĩna Mai Jin ƙai ne, Mai nũna sõyayya." |
|
1564 | 11 | 91 | قالوا يا شعيب ما نفقه كثيرا مما تقول وإنا لنراك فينا ضعيفا ولولا رهطك لرجمناك وما أنت علينا بعزيز |
| | | Suka ce: "Yã Shu'aibu! Bã mu fahimta da yawa daga abin da kake faɗi, kuma munã ganin ka mai rauni a cikinmu. Kuma bã dõmin jama'arka ba dã mun jẽfe ka, sabõda ba ka zama mai daraja a gunmu ba." |
|
1565 | 11 | 92 | قال يا قوم أرهطي أعز عليكم من الله واتخذتموه وراءكم ظهريا إن ربي بما تعملون محيط |
| | | Ya ce: "Ya mutãnena! Ashe, jama'ãta ce mafi daraja a gare ku daga Allah, kuma kun riƙẽ Shi a bãyanku abin jẽfarwa? Lallene Ubangijĩna Mai kẽwayẽwa nega abin da kuke aikatãwa." |
|
1566 | 11 | 93 | ويا قوم اعملوا على مكانتكم إني عامل سوف تعلمون من يأتيه عذاب يخزيه ومن هو كاذب وارتقبوا إني معكم رقيب |
| | | "Kuma ya mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku. Lalle nĩmai aiki ne. Da sannu zã ku san wãne ne azãba zã ta zo masa, ta wulakanta shi, kuma wãne ne maƙaryaci. Kuma ku yi jiran dãko, lalle ni mai dãko ne tãre da ku." |
|
1567 | 11 | 94 | ولما جاء أمرنا نجينا شعيبا والذين آمنوا معه برحمة منا وأخذت الذين ظلموا الصيحة فأصبحوا في ديارهم جاثمين |
| | | Kuma a lõkacin da umurninMu yã je, Muka kuɓutar da Shu'aibu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare, Mu. Kuma tsãwa ta kama waɗanda suka yi zãlunci. Sai suka wãyi gari guggurfãne a cikin gidãjensu. |
|
1568 | 11 | 95 | كأن لم يغنوا فيها ألا بعدا لمدين كما بعدت ثمود |
| | | Kamar ba su zaunã ba a cikinsu. To, halaka ta tabbata ga Madyana kamar yadda Samũdãwa suka halaka. |
|
1569 | 11 | 96 | ولقد أرسلنا موسى بآياتنا وسلطان مبين |
| | | Kuma haƙĩƙa Mun aiki Mũsã da ãyõyinMu, da dalĩli bayyananne. |
|