نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1308 | 9 | 73 | يا أيها النبي جاهد الكفار والمنافقين واغلظ عليهم ومأواهم جهنم وبئس المصير |
| | | Ya kai Annabi! Ka yãƙi kãfirai da munãfukai kuma ka tsaurara a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce. Tir da ta zama makõmar! |
|
1309 | 9 | 74 | يحلفون بالله ما قالوا ولقد قالوا كلمة الكفر وكفروا بعد إسلامهم وهموا بما لم ينالوا وما نقموا إلا أن أغناهم الله ورسوله من فضله فإن يتوبوا يك خيرا لهم وإن يتولوا يعذبهم الله عذابا أليما في الدنيا والآخرة وما لهم في الأرض من ولي ولا نصير |
| | | Sunã rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhãli kuwa lalle ne, haƙĩƙa, sun faɗi kalmar kãfirci, kuma; sun kãfirta a bãyan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga abin da ba su sãmu ba. Kuma ba su zargi kõme ba fãce dõmin Allah da ManzonSa Ya wadãtar da su daga falalarSa. To, idan sun tũba zai kasance mafi alhẽri gare su, kuma idan sun jũya bãya, Allah zaiazabtã su da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wani masõyi kõ wani mataimaki a cikin kasa. |
|
1310 | 9 | 75 | ومنهم من عاهد الله لئن آتانا من فضله لنصدقن ولنكونن من الصالحين |
| | | Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, "Lalle ne idan ya kãwo mana daga falalarSa, haƙĩƙa, munãbãyar da sadaka, kuma lalle ne munã kasancẽwa, daga sãlihai." |
|
1311 | 9 | 76 | فلما آتاهم من فضله بخلوا به وتولوا وهم معرضون |
| | | To, a lõkacin da Ya bã su daga falalarSa, sai suka yi rõwa da shi, kuma suka jũya bãya sunã mãsu bijirẽwa, |
|
1312 | 9 | 77 | فأعقبهم نفاقا في قلوبهم إلى يوم يلقونه بما أخلفوا الله ما وعدوه وبما كانوا يكذبون |
| | | Sai Ya biyar musu da munãfunci a cikin zukatansu har zuwa ga Rãnar da suke haɗuwa da Shi sabõda sãɓã wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma sabõda abin da suka kasance sunã yi na ƙarya. |
|
1313 | 9 | 78 | ألم يعلموا أن الله يعلم سرهم ونجواهم وأن الله علام الغيوب |
| | | Shin, ba su sani ba cẽwa lalle ne Allah Yanã sanin asĩrinsuda gãnawarsu, kuma lalle Allah ne Masanin abũbuwan fake? |
|
1314 | 9 | 79 | الذين يلمزون المطوعين من المؤمنين في الصدقات والذين لا يجدون إلا جهدهم فيسخرون منهم سخر الله منهم ولهم عذاب أليم |
| | | Waɗanda suke aibanta mãsu yin alhẽri daga mummunaia cikin dũkiyõyin sadaka, da waɗanda ba su sãmu fãce iyãkar ƙõƙarinsu, sai sanã yi musu izgili. Allah Yanã yin izgili gare su. Kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. |
|
1315 | 9 | 80 | استغفر لهم أو لا تستغفر لهم إن تستغفر لهم سبعين مرة فلن يغفر الله لهم ذلك بأنهم كفروا بالله ورسوله والله لا يهدي القوم الفاسقين |
| | | Kõ kã nẽma musu gãfara ko ba ka nẽma musu ba, idan ka nẽma musu gãfara sau saba'in, to, Allah bã zai gãfarta musu ba. Sabõda sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne fãsiƙai. |
|
1316 | 9 | 81 | فرح المخلفون بمقعدهم خلاف رسول الله وكرهوا أن يجاهدوا بأموالهم وأنفسهم في سبيل الله وقالوا لا تنفروا في الحر قل نار جهنم أشد حرا لو كانوا يفقهون |
| | | Waɗanda aka bari sun yi farin ciki da zamansu a bãyan Manzon Allah, kuma suka ƙi su yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu a cikin hanyar Allah, kuma suka ce: "Kada ku fita zuwa yãƙi a cikin zãfi."Ka ce: "Wutar Jahannama ce mafi tsanlnin zãfi." Dã sun kasance sunã fahimta! |
|
1317 | 9 | 82 | فليضحكوا قليلا وليبكوا كثيرا جزاء بما كانوا يكسبون |
| | | Sabõda haka su yi dãriya kaɗan, kuma su yi kũkada yawa a kan sãkamako ga abin da suka kasance sunã tsirfatãwa. |
|