نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1268 | 9 | 33 | هو الذي أرسل رسوله بالهدى ودين الحق ليظهره على الدين كله ولو كره المشركون |
| | | Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, dõmin ya bayyanl shi a kan addini dukansa, kuma kõ dã mushirikai sun ƙi. |
|
1269 | 9 | 34 | يا أيها الذين آمنوا إن كثيرا من الأحبار والرهبان ليأكلون أموال الناس بالباطل ويصدون عن سبيل الله والذين يكنزون الذهب والفضة ولا ينفقونها في سبيل الله فبشرهم بعذاب أليم |
| | | Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. |
|
1270 | 9 | 35 | يوم يحمى عليها في نار جهنم فتكوى بها جباههم وجنوبهم وظهورهم هذا ما كنزتم لأنفسكم فذوقوا ما كنتم تكنزون |
| | | A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a taska." |
|
1271 | 9 | 36 | إن عدة الشهور عند الله اثنا عشر شهرا في كتاب الله يوم خلق السماوات والأرض منها أربعة حرم ذلك الدين القيم فلا تظلموا فيهن أنفسكم وقاتلوا المشركين كافة كما يقاتلونكم كافة واعلموا أن الله مع المتقين |
| | | Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa. |
|
1272 | 9 | 37 | إنما النسيء زيادة في الكفر يضل به الذين كفروا يحلونه عاما ويحرمونه عاما ليواطئوا عدة ما حرم الله فيحلوا ما حرم الله زين لهم سوء أعمالهم والله لا يهدي القوم الكافرين |
| | | Abin sani kawai, "Jinkirtãwa" ƙãri ne a cikin kãfirci, anã ɓatar da waɗanda suka kãfirta game da shi. Sunã halattar da watã a wata shẽkara kuma su haramtar da shi a wata shẽkara dõmin su dãce da adadin abin da Allah Ya haramta. Sabõda haka sunã halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawãce musu mũnanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai. |
|
1273 | 9 | 38 | يا أيها الذين آمنوا ما لكم إذا قيل لكم انفروا في سبيل الله اثاقلتم إلى الأرض أرضيتم بالحياة الدنيا من الآخرة فما متاع الحياة الدنيا في الآخرة إلا قليل |
| | | Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yãƙi a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin Lãhira, fãce kaɗan. |
|
1274 | 9 | 39 | إلا تنفروا يعذبكم عذابا أليما ويستبدل قوما غيركم ولا تضروه شيئا والله على كل شيء قدير |
| | | Idan ba ku fita da yãƙi ba, Allah zai azabta ku da azãba mai raɗaɗi, kuma Ya musanya wasu mutãne, wasunku (a maimakonku). Kuma bã zã ku cũtar da Shida kõme ba. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne. |
|
1275 | 9 | 40 | إلا تنصروه فقد نصره الله إذ أخرجه الذين كفروا ثاني اثنين إذ هما في الغار إذ يقول لصاحبه لا تحزن إن الله معنا فأنزل الله سكينته عليه وأيده بجنود لم تروها وجعل كلمة الذين كفروا السفلى وكلمة الله هي العليا والله عزيز حكيم |
| | | Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: "Kada ka yi baƙin ciki, lalle ne Allah Yanã tãre da mu." Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar waɗanda suka kãfirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima. |
|
1276 | 9 | 41 | انفروا خفافا وثقالا وجاهدوا بأموالكم وأنفسكم في سبيل الله ذلكم خير لكم إن كنتم تعلمون |
| | | Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani. |
|
1277 | 9 | 42 | لو كان عرضا قريبا وسفرا قاصدا لاتبعوك ولكن بعدت عليهم الشقة وسيحلفون بالله لو استطعنا لخرجنا معكم يهلكون أنفسهم والله يعلم إنهم لكاذبون |
| | | Dã yã kasance wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa. Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah, "Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku." Sunã halakar da kansu (da rantsuwar ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.' |
|