نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
993 | 7 | 39 | وقالت أولاهم لأخراهم فما كان لكم علينا من فضل فذوقوا العذاب بما كنتم تكسبون |
| | | Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, bã ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azãba sabõda abin da kuka kasance kunã tãrãwa!" |
|
994 | 7 | 40 | إن الذين كذبوا بآياتنا واستكبروا عنها لا تفتح لهم أبواب السماء ولا يدخلون الجنة حتى يلج الجمل في سم الخياط وكذلك نجزي المجرمين |
| | | Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi. |
|
995 | 7 | 41 | لهم من جهنم مهاد ومن فوقهم غواش وكذلك نجزي الظالمين |
| | | Sunã da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa azzãlumai. |
|
996 | 7 | 42 | والذين آمنوا وعملوا الصالحات لا نكلف نفسا إلا وسعها أولئك أصحاب الجنة هم فيها خالدون |
| | | Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne. |
|
997 | 7 | 43 | ونزعنا ما في صدورهم من غل تجري من تحتهم الأنهار وقالوا الحمد لله الذي هدانا لهذا وما كنا لنهتدي لولا أن هدانا الله لقد جاءت رسل ربنا بالحق ونودوا أن تلكم الجنة أورثتموها بما كنتم تعملون |
| | | Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cẽwa: "Waccan Aljlnna an gãdar da ku ita, sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa." |
|
998 | 7 | 44 | ونادى أصحاب الجنة أصحاب النار أن قد وجدنا ما وعدنا ربنا حقا فهل وجدتم ما وعد ربكم حقا قالوا نعم فأذن مؤذن بينهم أن لعنة الله على الظالمين |
| | | Kuma 'yan Aljanna suka kirãyi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai." |
|
999 | 7 | 45 | الذين يصدون عن سبيل الله ويبغونها عوجا وهم بالآخرة كافرون |
| | | "Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne." |
|
1000 | 7 | 46 | وبينهما حجاب وعلى الأعراف رجال يعرفون كلا بسيماهم ونادوا أصحاب الجنة أن سلام عليكم لم يدخلوها وهم يطمعون |
| | | Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki, kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni. |
|
1001 | 7 | 47 | وإذا صرفت أبصارهم تلقاء أصحاب النار قالوا ربنا لا تجعلنا مع القوم الظالمين |
| | | Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abõkan wuta, su ce: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu tãre da mutãne azzãlumai." |
|
1002 | 7 | 48 | ونادى أصحاب الأعراف رجالا يعرفونهم بسيماهم قالوا ما أغنى عنكم جمعكم وما كنتم تستكبرون |
| | | Kuma abõkan A'araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce: "Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba daga barinku?" |
|