نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
974 | 7 | 20 | فوسوس لهما الشيطان ليبدي لهما ما ووري عنهما من سوآتهما وقال ما نهاكما ربكما عن هذه الشجرة إلا أن تكونا ملكين أو تكونا من الخالدين |
| | | Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama." |
|
975 | 7 | 21 | وقاسمهما إني لكما لمن الناصحين |
| | | Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne. |
|
976 | 7 | 22 | فدلاهما بغرور فلما ذاقا الشجرة بدت لهما سوآتهما وطفقا يخصفان عليهما من ورق الجنة وناداهما ربهما ألم أنهكما عن تلكما الشجرة وأقل لكما إن الشيطان لكما عدو مبين |
| | | Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?" |
|
977 | 7 | 23 | قالا ربنا ظلمنا أنفسنا وإن لم تغفر لنا وترحمنا لنكونن من الخاسرين |
| | | Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra." |
|
978 | 7 | 24 | قال اهبطوا بعضكم لبعض عدو ولكم في الأرض مستقر ومتاع إلى حين |
| | | Ya ce: "Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi." |
|
979 | 7 | 25 | قال فيها تحيون وفيها تموتون ومنها تخرجون |
| | | Ya ce: "A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku." |
|
980 | 7 | 26 | يا بني آدم قد أنزلنا عليكم لباسا يواري سوآتكم وريشا ولباس التقوى ذلك خير ذلك من آيات الله لعلهم يذكرون |
| | | Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa! |
|
981 | 7 | 27 | يا بني آدم لا يفتننكم الشيطان كما أخرج أبويكم من الجنة ينزع عنهما لباسهما ليريهما سوآتهما إنه يراكم هو وقبيله من حيث لا ترونهم إنا جعلنا الشياطين أولياء للذين لا يؤمنون |
| | | Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni. |
|
982 | 7 | 28 | وإذا فعلوا فاحشة قالوا وجدنا عليها آباءنا والله أمرنا بها قل إن الله لا يأمر بالفحشاء أتقولون على الله ما لا تعلمون |
| | | Kuma idan suka aikata alfãsha su ce: "Mun sãmi ubanninmu akanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah?" |
|
983 | 7 | 29 | قل أمر ربي بالقسط وأقيموا وجوهكم عند كل مسجد وادعوه مخلصين له الدين كما بدأكم تعودون |
| | | Ka ce: "Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙẽ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa." |
|