نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
948 | 6 | 159 | إن الذين فرقوا دينهم وكانوا شيعا لست منهم في شيء إنما أمرهم إلى الله ثم ينبئهم بما كانوا يفعلون |
| | | Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa. |
|
949 | 6 | 160 | من جاء بالحسنة فله عشر أمثالها ومن جاء بالسيئة فلا يجزى إلا مثلها وهم لا يظلمون |
| | | Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to, yanã da gõma ɗin misãlansa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, bã zã a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma sũ bã a zãluntar su. |
|
950 | 6 | 161 | قل إنني هداني ربي إلى صراط مستقيم دينا قيما ملة إبراهيم حنيفا وما كان من المشركين |
| | | Ka ce: "Lalle nĩ, Ubangijina Yã shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addĩni, ƙĩmantãwa (ga abũbuwa), mai aƙĩdar Ibrãhĩm, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba." |
|
951 | 6 | 162 | قل إن صلاتي ونسكي ومحياي ومماتي لله رب العالمين |
| | | Ka ce: "Lalle ne sallãta, da baikõna, da rãyuwãta, da mutuwãta, na Allah ne Ubangijin tãlikai." |
|
952 | 6 | 163 | لا شريك له وبذلك أمرت وأنا أول المسلمين |
| | | "Bãbu abõkin tãrayya a gare Shi. Kuma da wancan aka umurce ni, kuma ni ne farkon mãsu sallamãwa." |
|
953 | 6 | 164 | قل أغير الله أبغي ربا وهو رب كل شيء ولا تكسب كل نفس إلا عليها ولا تزر وازرة وزر أخرى ثم إلى ربكم مرجعكم فينبئكم بما كنتم فيه تختلفون |
| | | Ka ce: "Shin wanin Allah nake nẽma ya zama Ubangiji, alhãli kuwa Shĩ ne Ubangijin dukan kõme? Kuma wani rai bã ya yin tsirfa fãce dõmin kansa, kuma mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani, sa'an nan kuma kõmawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Yã bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũnã?" |
|
954 | 6 | 165 | وهو الذي جعلكم خلائف الأرض ورفع بعضكم فوق بعض درجات ليبلوكم في ما آتاكم إن ربك سريع العقاب وإنه لغفور رحيم |
| | | "Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya ku mãsu maye wa jũnaga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sãshenku bisa ga sãshe da darajõji; dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku." Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggãwar uƙkũba ne, kuma lalle ne Shi, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. |
|
955 | 7 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم المص |
| | | A. L̃. M̃. Ṣ̃. |
|
956 | 7 | 2 | كتاب أنزل إليك فلا يكن في صدرك حرج منه لتنذر به وذكرى للمؤمنين |
| | | Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai. |
|
957 | 7 | 3 | اتبعوا ما أنزل إليكم من ربكم ولا تتبعوا من دونه أولياء قليلا ما تذكرون |
| | | Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa. |
|