نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
839 | 6 | 50 | قل لا أقول لكم عندي خزائن الله ولا أعلم الغيب ولا أقول لكم إني ملك إن أتبع إلا ما يوحى إلي قل هل يستوي الأعمى والبصير أفلا تتفكرون |
| | | Ka ce: "Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni malã'ika ne. Ba ni bi, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni." Ka ce: "Shin, makãho da mai gani sunã daidaita? Shin fa, ba ku yin tunãni?" |
|
840 | 6 | 51 | وأنذر به الذين يخافون أن يحشروا إلى ربهم ليس لهم من دونه ولي ولا شفيع لعلهم يتقون |
| | | Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsõron a tãra su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani masõyi baicinSa, kuma babu mai cẽto, tsammãninsu, sunã yin taƙawa. |
|
841 | 6 | 52 | ولا تطرد الذين يدعون ربهم بالغداة والعشي يريدون وجهه ما عليك من حسابهم من شيء وما من حسابك عليهم من شيء فتطردهم فتكون من الظالمين |
| | | Kuma kada ka kõri waɗanda suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai. |
|
842 | 6 | 53 | وكذلك فتنا بعضهم ببعض ليقولوا أهؤلاء من الله عليهم من بيننا أليس الله بأعلم بالشاكرين |
| | | Kuma kamar wannan ne, Muka fitini sãshensu da sãshe, dõmin su ce: "Shin waɗannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakãninmu?" Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga mãsu gõdiya? |
|
843 | 6 | 54 | وإذا جاءك الذين يؤمنون بآياتنا فقل سلام عليكم كتب ربكم على نفسه الرحمة أنه من عمل منكم سوءا بجهالة ثم تاب من بعده وأصلح فأنه غفور رحيم |
| | | Kuma idan waɗanda suke yin ĩmãni da ãyõyinMu suka jẽ maka, sai ka ce: "Aminci ya tabbata a gareku; Ubangjinku Ya wajabta rahama ga kanSa, cẽwa lalle ne wanda ya aikata aibi da jãhilci daga cikinku, sa'an nan kuma ya tũba daga bãyansa, kuma ya gyãra, to, lalle Shi, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." |
|
844 | 6 | 55 | وكذلك نفصل الآيات ولتستبين سبيل المجرمين |
| | | Kuma kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, kuma dõmin hanyar mãsu laifi ta bayyana. |
|
845 | 6 | 56 | قل إني نهيت أن أعبد الذين تدعون من دون الله قل لا أتبع أهواءكم قد ضللت إذا وما أنا من المهتدين |
| | | Ka ce: "Lalle ne ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira daga baicin Allah." Ka cc: "Ba ni bin son zũciyõyinku, (dõmin in nã yi haka) lalle ne, nã ɓace. A sa'an nan, kuma ban zama daga shiryayyu ba." |
|
846 | 6 | 57 | قل إني على بينة من ربي وكذبتم به ما عندي ما تستعجلون به إن الحكم إلا لله يقص الحق وهو خير الفاصلين |
| | | Ka ce: "Lalle ne inã kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da Shi; abin da kuke nẽman gaugãwarsa, bã ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba fãce, ga Allah, Yanã bãyar da lãbãrin gaskiya, kuma shĩ ne mafi alhẽrin mãsu rarrabẽwa." |
|
847 | 6 | 58 | قل لو أن عندي ما تستعجلون به لقضي الأمر بيني وبينكم والله أعلم بالظالمين |
| | | Ka ce: "Lalle ne, dã a wurina akwai abin da kuke nẽman gaugãwa da shi, haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin, a tsakãnina da tsakãninku, kuma Allah Shĩ ne Mafi sani ga azzũlumai." |
|
848 | 6 | 59 | وعنده مفاتح الغيب لا يعلمها إلا هو ويعلم ما في البر والبحر وما تسقط من ورقة إلا يعلمها ولا حبة في ظلمات الأرض ولا رطب ولا يابس إلا في كتاب مبين |
| | | Kuma a wurinSa mabũdan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa. |
|