نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
805 | 6 | 16 | من يصرف عنه يومئذ فقد رحمه وذلك الفوز المبين |
| | | "Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rãnar, to, lalle ne, (Allah) Yã yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya." |
|
806 | 6 | 17 | وإن يمسسك الله بضر فلا كاشف له إلا هو وإن يمسسك بخير فهو على كل شيء قدير |
| | | "Idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, fãce Shĩ, kuma idanYa shãfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kõme, Mai ĩkon yi." |
|
807 | 6 | 18 | وهو القاهر فوق عباده وهو الحكيم الخبير |
| | | "Kuma Shĩ ne mai Tanƙwasa a kan bayinSa, kuma Shi ne Mai hikima, Masani." |
|
808 | 6 | 19 | قل أي شيء أكبر شهادة قل الله شهيد بيني وبينكم وأوحي إلي هذا القرآن لأنذركم به ومن بلغ أئنكم لتشهدون أن مع الله آلهة أخرى قل لا أشهد قل إنما هو إله واحد وإنني بريء مما تشركون |
| | | Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa, kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bã zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki." |
|
809 | 6 | 20 | الذين آتيناهم الكتاب يعرفونه كما يعرفون أبناءهم الذين خسروا أنفسهم فهم لا يؤمنون |
| | | Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni. |
|
810 | 6 | 21 | ومن أظلم ممن افترى على الله كذبا أو كذب بآياته إنه لا يفلح الظالمون |
| | | Wãne ne mafi zãlunci daga wanda yake ƙirƙira karya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinsa? Lalle ne shĩ, azzalumai bã zã su ci nasara ba. |
|
811 | 6 | 22 | ويوم نحشرهم جميعا ثم نقول للذين أشركوا أين شركاؤكم الذين كنتم تزعمون |
| | | Kuma rãnar da Muka tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Mu ce wa waɗanda suka yi shirki: "Inã abõkan tãrayyarku waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?" |
|
812 | 6 | 23 | ثم لم تكن فتنتهم إلا أن قالوا والله ربنا ما كنا مشركين |
| | | Sa'an nan kuma fitinarsu ba ta kasance ba, fãce dõmin sun ce: "Munã rantsuwa da Allah Ubangijinmu, ba mu kasance mãsu yin shirki ba." |
|
813 | 6 | 24 | انظر كيف كذبوا على أنفسهم وضل عنهم ما كانوا يفترون |
| | | Ka dũba yadda suka ƙaryata kansu! Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙira ƙaryarsa, ya ɓace daga gare su. |
|
814 | 6 | 25 | ومنهم من يستمع إليك وجعلنا على قلوبهم أكنة أن يفقهوه وفي آذانهم وقرا وإن يروا كل آية لا يؤمنوا بها حتى إذا جاءوك يجادلونك يقول الذين كفروا إن هذا إلا أساطير الأولين |
| | | Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurãre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi. Kuma idan sun ga kõwace ãyã bã zã su yi ĩmãni da ita ba har idan sunjẽ maka sunã jãyayya da kai, waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko." |
|