نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
799 | 6 | 10 | ولقد استهزئ برسل من قبلك فحاق بالذين سخروا منهم ما كانوا به يستهزئون |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da manzanni daga gabaninka, sai waɗanda suka yi izgilin, abin da suka kasance sunã izgili da shi ya fãɗa musu. |
|
800 | 6 | 11 | قل سيروا في الأرض ثم انظروا كيف كان عاقبة المكذبين |
| | | Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance." |
|
801 | 6 | 12 | قل لمن ما في السماوات والأرض قل لله كتب على نفسه الرحمة ليجمعنكم إلى يوم القيامة لا ريب فيه الذين خسروا أنفسهم فهم لا يؤمنون |
| | | Ka ce: "Na wãne ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Na Allah ne." Yã wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yanã tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, babu shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ ba zã su yi ĩmani ba." |
|
802 | 6 | 13 | وله ما سكن في الليل والنهار وهو السميع العليم |
| | | "Kuma Shĩ ne da mallakar abin da ya yi kawaici a cikin dare da yini, kuma Shi ne Mai ji, Masani." |
|
803 | 6 | 14 | قل أغير الله أتخذ وليا فاطر السماوات والأرض وهو يطعم ولا يطعم قل إني أمرت أن أكون أول من أسلم ولا تكونن من المشركين |
| | | Ka ce: "Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, (alhãli Allah ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yanã ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi?" Ka ce: "Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga mãsu shirki." |
|
804 | 6 | 15 | قل إني أخاف إن عصيت ربي عذاب يوم عظيم |
| | | Kace: "Lalle ne nĩ inã tsõron azãbar Yini Mai girma, idan nã sãɓã wa Ubangijina." |
|
805 | 6 | 16 | من يصرف عنه يومئذ فقد رحمه وذلك الفوز المبين |
| | | "Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rãnar, to, lalle ne, (Allah) Yã yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya." |
|
806 | 6 | 17 | وإن يمسسك الله بضر فلا كاشف له إلا هو وإن يمسسك بخير فهو على كل شيء قدير |
| | | "Idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, fãce Shĩ, kuma idanYa shãfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kõme, Mai ĩkon yi." |
|
807 | 6 | 18 | وهو القاهر فوق عباده وهو الحكيم الخبير |
| | | "Kuma Shĩ ne mai Tanƙwasa a kan bayinSa, kuma Shi ne Mai hikima, Masani." |
|
808 | 6 | 19 | قل أي شيء أكبر شهادة قل الله شهيد بيني وبينكم وأوحي إلي هذا القرآن لأنذركم به ومن بلغ أئنكم لتشهدون أن مع الله آلهة أخرى قل لا أشهد قل إنما هو إله واحد وإنني بريء مما تشركون |
| | | Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa, kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bã zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki." |
|