نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
78 | 2 | 71 | قال إنه يقول إنها بقرة لا ذلول تثير الأرض ولا تسقي الحرث مسلمة لا شية فيها قالوا الآن جئت بالحق فذبحوها وما كادوا يفعلون |
| | | Ya ce: "Lalle ne Shi, Yana cẽwa: "Ita wata sãniya ce; ba horarra bã tana noman ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lãfiyayya ce: bãbu wani sõfane a cikinta." Suka ce: "Yanzu kã zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba zã su aikata ba. |
|
79 | 2 | 72 | وإذ قتلتم نفسا فادارأتم فيها والله مخرج ما كنتم تكتمون |
| | | Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa, kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne. |
|
80 | 2 | 73 | فقلنا اضربوه ببعضها كذلك يحيي الله الموتى ويريكم آياته لعلكم تعقلون |
| | | Sai Muka ce: "Ku dõke shi da wani sãshenta." Kamar wancan ne Allah Yake rãyar da matattu, kuma Ya nũna muku ayõyinSa, tsammãninku kuna hankalta. |
|
81 | 2 | 74 | ثم قست قلوبكم من بعد ذلك فهي كالحجارة أو أشد قسوة وإن من الحجارة لما يتفجر منه الأنهار وإن منها لما يشقق فيخرج منه الماء وإن منها لما يهبط من خشية الله وما الله بغافل عما تعملون |
| | | San'nan kuma zukãtanku, suka ƙẽƙashe daga bãyan wancan. Sabõda haka suka zamanto kamar duwatsu. Ko mafi tsananin ƙeƙashewa. kuma lalle ne daga duwãtsu, haƙĩka, akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su, haƙĩƙa, akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi, kuma lalle ne, haƙĩƙa, daga gare su, haƙĩƙa, akwai da yake fãɗõwa dõmin tsõron Allah, kuma Allah bai zama gãfili ba daga barin abin da kuke aikatãwa. |
|
82 | 2 | 75 | أفتطمعون أن يؤمنوا لكم وقد كان فريق منهم يسمعون كلام الله ثم يحرفونه من بعد ما عقلوه وهم يعلمون |
| | | Shin fa kuna tsammãnin zã su yi imãni sabõda ku, alhãli kuwa, haƙĩƙa, wata ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su karkatar da ita daga bãyan sun gãne ta, alhãli sũ, suna sane? |
|
83 | 2 | 76 | وإذا لقوا الذين آمنوا قالوا آمنا وإذا خلا بعضهم إلى بعض قالوا أتحدثونهم بما فتح الله عليكم ليحاجوكم به عند ربكم أفلا تعقلون |
| | | Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni sukan ce: "Mun yi ĩmãni," kuma idan sãshensu ya wõfinta zuwa ga sãshe, sukan ce: "Shin, kuna yi musu magana da abin da Allah Ya buɗa muku ne dõmin su yi muku hujja da shi a wurin Ubangijinku?" Shin fa, bã ku hankalta? |
|
84 | 2 | 77 | أولا يعلمون أن الله يعلم ما يسرون وما يعلنون |
| | | Shin, kuma bã su sanin cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da suke ɓõyẽwa da abin da suke bayyanãwa? |
|
85 | 2 | 78 | ومنهم أميون لا يعلمون الكتاب إلا أماني وإن هم إلا يظنون |
| | | Kuma daga cikinsu akwai ummiyyai, bã su da sanin Littãfi, fãce tãtsuniyoyi, kuma sũ bã kõme suke yi ba fãce suna yin zato. |
|
86 | 2 | 79 | فويل للذين يكتبون الكتاب بأيديهم ثم يقولون هذا من عند الله ليشتروا به ثمنا قليلا فويل لهم مما كتبت أيديهم وويل لهم مما يكسبون |
| | | To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sanã'antãwa. |
|
87 | 2 | 80 | وقالوا لن تمسنا النار إلا أياما معدودة قل أتخذتم عند الله عهدا فلن يخلف الله عهده أم تقولون على الله ما لا تعلمون |
| | | Kuma suka ce: "Wuta bã zã ta shãfe mu ba, fãce, 'yan kwãnuka ƙidãyayyu."Ka ce: "Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai sãɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah?" |
|