نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
756 | 5 | 87 | يا أيها الذين آمنوا لا تحرموا طيبات ما أحل الله لكم ولا تعتدوا إن الله لا يحب المعتدين |
| | | Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku haramta abubuwa mãsu dãɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bã Ya son mãsu ƙetare haddi. |
|
757 | 5 | 88 | وكلوا مما رزقكم الله حلالا طيبا واتقوا الله الذي أنتم به مؤمنون |
| | | Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake ku, mãsu ĩmãni ne da shi. |
|
758 | 5 | 89 | لا يؤاخذكم الله باللغو في أيمانكم ولكن يؤاخذكم بما عقدتم الأيمان فكفارته إطعام عشرة مساكين من أوسط ما تطعمون أهليكم أو كسوتهم أو تحرير رقبة فمن لم يجد فصيام ثلاثة أيام ذلك كفارة أيمانكم إذا حلفتم واحفظوا أيمانكم كذلك يبين الله لكم آياته لعلكم تشكرون |
| | | Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa 'yantãwar wuya. Sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa. |
|
759 | 5 | 90 | يا أيها الذين آمنوا إنما الخمر والميسر والأنصاب والأزلام رجس من عمل الشيطان فاجتنبوه لعلكم تفلحون |
| | | Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara. |
|
760 | 5 | 91 | إنما يريد الشيطان أن يوقع بينكم العداوة والبغضاء في الخمر والميسر ويصدكم عن ذكر الله وعن الصلاة فهل أنتم منتهون |
| | | Abin sani kawaĩ Shaiɗan yanã nufin ya aukar da adãwa da ƙeta a tsakãninku, a cikin giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne? |
|
761 | 5 | 92 | وأطيعوا الله وأطيعوا الرسول واحذروا فإن توليتم فاعلموا أنما على رسولنا البلاغ المبين |
| | | Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo, kuma ku kiyãye. To, idan kun jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, iyarwa bayyananniya. |
|
762 | 5 | 93 | ليس على الذين آمنوا وعملوا الصالحات جناح فيما طعموا إذا ما اتقوا وآمنوا وعملوا الصالحات ثم اتقوا وآمنوا ثم اتقوا وأحسنوا والله يحب المحسنين |
| | | Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa. |
|
763 | 5 | 94 | يا أيها الذين آمنوا ليبلونكم الله بشيء من الصيد تناله أيديكم ورماحكم ليعلم الله من يخافه بالغيب فمن اعتدى بعد ذلك فله عذاب أليم |
| | | Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi. |
|
764 | 5 | 95 | يا أيها الذين آمنوا لا تقتلوا الصيد وأنتم حرم ومن قتله منكم متعمدا فجزاء مثل ما قتل من النعم يحكم به ذوا عدل منكم هديا بالغ الكعبة أو كفارة طعام مساكين أو عدل ذلك صياما ليذوق وبال أمره عفا الله عما سلف ومن عاد فينتقم الله منه والله عزيز ذو انتقام |
| | | Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa. |
|
765 | 5 | 96 | أحل لكم صيد البحر وطعامه متاعا لكم وللسيارة وحرم عليكم صيد البر ما دمتم حرما واتقوا الله الذي إليه تحشرون |
| | | An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dõmin jin dãɗi a gare ku, kuma dõmin matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama mãsu harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tãra ku. |
|