نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
626 | 4 | 133 | إن يشأ يذهبكم أيها الناس ويأت بآخرين وكان الله على ذلك قديرا |
| | | Idan Yã so, zã Ya tafi da ku, yã kũ mutãne! kuma Ya zo da wasu. Allah Yã kasance a kan haka, Mai ĩkon yi ne. |
|
627 | 4 | 134 | من كان يريد ثواب الدنيا فعند الله ثواب الدنيا والآخرة وكان الله سميعا بصيرا |
| | | Wanda ya kasance Yanã nufin sakamakon dũniya, to, a wurin Allah sakamakon dũniya da Lãhira yake. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Mai gani. |
|
628 | 4 | 135 | يا أيها الذين آمنوا كونوا قوامين بالقسط شهداء لله ولو على أنفسكم أو الوالدين والأقربين إن يكن غنيا أو فقيرا فالله أولى بهما فلا تتبعوا الهوى أن تعدلوا وإن تلووا أو تعرضوا فإن الله كان بما تعملون خبيرا |
| | | Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa. |
|
629 | 4 | 136 | يا أيها الذين آمنوا آمنوا بالله ورسوله والكتاب الذي نزل على رسوله والكتاب الذي أنزل من قبل ومن يكفر بالله وملائكته وكتبه ورسله واليوم الآخر فقد ضل ضلالا بعيدا |
| | | Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni. To, wanda ya kãfirta da Allah da malã'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rãnar Lãhira, to, lalle ne yã ɓace, ɓata mai nĩsa. |
|
630 | 4 | 137 | إن الذين آمنوا ثم كفروا ثم آمنوا ثم كفروا ثم ازدادوا كفرا لم يكن الله ليغفر لهم ولا ليهديهم سبيلا |
| | | Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sa'an nan kuma suka yi ĩmani, sa'an nan kuma suka kãfirta sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci, Allah bai kasance Yanã gãfarta musu ba, kuma bã zai shiryar da su ga hanya ba. |
|
631 | 4 | 138 | بشر المنافقين بأن لهم عذابا أليما |
| | | Ka yi wa munãfukai bushãra da cẽwa lalle ne sunã da azãba mai raɗaɗi. |
|
632 | 4 | 139 | الذين يتخذون الكافرين أولياء من دون المؤمنين أيبتغون عندهم العزة فإن العزة لله جميعا |
| | | Waɗanda suke riƙon kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin sunã nẽman izza ne a wurinsu? To, lalle ne izza ga Allah take gabã ɗaya. |
|
633 | 4 | 140 | وقد نزل عليكم في الكتاب أن إذا سمعتم آيات الله يكفر بها ويستهزأ بها فلا تقعدوا معهم حتى يخوضوا في حديث غيره إنكم إذا مثلهم إن الله جامع المنافقين والكافرين في جهنم جميعا |
| | | Kuma lalle ne Yã sassaukar muku a cikin Littãfi cẽwa idan kun ji ãyõyin Allah, anã kãfirta da su, kuma anã izgili da su, to, kada ku zauna tãre da sũ, sai sun shiga cikin wani lãbãri. Lalle ne kũ, a lõkacin nan misãlinsu kuke. Lalle ne, Allah Mai tãra munãfukai da kãfirai ne a cikin Jahannama gabã ɗaya. |
|
634 | 4 | 141 | الذين يتربصون بكم فإن كان لكم فتح من الله قالوا ألم نكن معكم وإن كان للكافرين نصيب قالوا ألم نستحوذ عليكم ونمنعكم من المؤمنين فالله يحكم بينكم يوم القيامة ولن يجعل الله للكافرين على المؤمنين سبيلا |
| | | Waɗanda suke jiran dãko game da ku; har idan wata nasara daga Allah ta kasance a gare ku, sai su ce: "Ashe, ba mu kasance tãre da kũ ba?" Kuma idan wani rabo ya sãmu ga kãfirai sai su ce: "Ashe ba mu rinjãye ku ba, kuma muka tsare ku daga mũminai?" To, Allah ne Yake yin hukunci tsakãninku a Rãnar ¡iyãma, kuma Allah bã zai sanya hanya ba ga kãfirai a kan mũminai. |
|
635 | 4 | 142 | إن المنافقين يخادعون الله وهو خادعهم وإذا قاموا إلى الصلاة قاموا كسالى يراءون الناس ولا يذكرون الله إلا قليلا |
| | | Lalle ne munãfukai sunã yaudarẽwa da Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga salla, sai su tãshi sunã mãsu kasãla. Suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan. |
|