نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
6176 | 102 | 8 | ثم لتسألن يومئذ عن النعيم |
| | | Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku). |
|
6177 | 103 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والعصر |
| | | Ina rantsuwa da zãmani. |
|
6178 | 103 | 2 | إن الإنسان لفي خسر |
| | | Lalle ne mutum yana a cikin hasara. |
|
6179 | 103 | 3 | إلا الذين آمنوا وعملوا الصالحات وتواصوا بالحق وتواصوا بالصبر |
| | | Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara). |
|
6180 | 104 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم ويل لكل همزة لمزة |
| | | Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa). |
|
6181 | 104 | 2 | الذي جمع مالا وعدده |
| | | Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa. |
|
6182 | 104 | 3 | يحسب أن ماله أخلده |
| | | Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi. |
|
6183 | 104 | 4 | كلا لينبذن في الحطمة |
| | | A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama. |
|
6184 | 104 | 5 | وما أدراك ما الحطمة |
| | | Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama? |
|
6185 | 104 | 6 | نار الله الموقدة |
| | | Wutar Allah ce wadda ake hurawa. |
|