نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
6159 | 101 | 2 | ما القارعة |
| | | Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa? |
|
6160 | 101 | 3 | وما أدراك ما القارعة |
| | | Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa? |
|
6161 | 101 | 4 | يوم يكون الناس كالفراش المبثوث |
| | | Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa. |
|
6162 | 101 | 5 | وتكون الجبال كالعهن المنفوش |
| | | Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe. |
|
6163 | 101 | 6 | فأما من ثقلت موازينه |
| | | To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi. |
|
6164 | 101 | 7 | فهو في عيشة راضية |
| | | To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda. |
|
6165 | 101 | 8 | وأما من خفت موازينه |
| | | Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi). |
|
6166 | 101 | 9 | فأمه هاوية |
| | | To, uwarsa Hãwiya ce. |
|
6167 | 101 | 10 | وما أدراك ما هيه |
| | | Kuma me ya sanar da kai mece ce ita? |
|
6168 | 101 | 11 | نار حامية |
| | | Wata wuta ce mai zafi. |
|