نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
6126 | 97 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم إنا أنزلناه في ليلة القدر |
| | | Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja) |
|
6127 | 97 | 2 | وما أدراك ما ليلة القدر |
| | | To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari? |
|
6128 | 97 | 3 | ليلة القدر خير من ألف شهر |
| | | Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu. |
|
6129 | 97 | 4 | تنزل الملائكة والروح فيها بإذن ربهم من كل أمر |
| | | Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni. |
|
6130 | 97 | 5 | سلام هي حتى مطلع الفجر |
| | | Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri. |
|
6131 | 98 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم لم يكن الذين كفروا من أهل الكتاب والمشركين منفكين حتى تأتيهم البينة |
| | | Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu. |
|
6132 | 98 | 2 | رسول من الله يتلو صحفا مطهرة |
| | | Wani Manzo daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki. |
|
6133 | 98 | 3 | فيها كتب قيمة |
| | | A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja. |
|
6134 | 98 | 4 | وما تفرق الذين أوتوا الكتاب إلا من بعد ما جاءتهم البينة |
| | | Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu. |
|
6135 | 98 | 5 | وما أمروا إلا ليعبدوا الله مخلصين له الدين حنفاء ويقيموا الصلاة ويؤتوا الزكاة وذلك دين القيمة |
| | | Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai. |
|