نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
6119 | 96 | 13 | أرأيت إن كذب وتولى |
| | | Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya? |
|
6120 | 96 | 14 | ألم يعلم بأن الله يرى |
| | | Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani? |
|
6121 | 96 | 15 | كلا لئن لم ينته لنسفعا بالناصية |
| | | A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa. |
|
6122 | 96 | 16 | ناصية كاذبة خاطئة |
| | | Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi. |
|
6123 | 96 | 17 | فليدع ناديه |
| | | Sai ya kirayi ƙungiyarsa. |
|
6124 | 96 | 18 | سندع الزبانية |
| | | Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma). |
|
6125 | 96 | 19 | كلا لا تطعه واسجد واقترب |
| | | A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka). |
|
6126 | 97 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم إنا أنزلناه في ليلة القدر |
| | | Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja) |
|
6127 | 97 | 2 | وما أدراك ما ليلة القدر |
| | | To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari? |
|
6128 | 97 | 3 | ليلة القدر خير من ألف شهر |
| | | Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu. |
|