نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
6052 | 91 | 9 | قد أفلح من زكاها |
| | | Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo. |
|
6053 | 91 | 10 | وقد خاب من دساها |
| | | Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe. |
|
6054 | 91 | 11 | كذبت ثمود بطغواها |
| | | Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu. |
|
6055 | 91 | 12 | إذ انبعث أشقاها |
| | | A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu). |
|
6056 | 91 | 13 | فقال لهم رسول الله ناقة الله وسقياها |
| | | Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!" |
|
6057 | 91 | 14 | فكذبوه فعقروها فدمدم عليهم ربهم بذنبهم فسواها |
| | | Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi). |
|
6058 | 91 | 15 | ولا يخاف عقباها |
| | | Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar). |
|
6059 | 92 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والليل إذا يغشى |
| | | Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa. |
|
6060 | 92 | 2 | والنهار إذا تجلى |
| | | Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa. |
|
6061 | 92 | 3 | وما خلق الذكر والأنثى |
| | | Da abin da ya halitta namiji da mace. |
|