نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
6006 | 89 | 13 | فصب عليهم ربك سوط عذاب |
| | | Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba. |
|
6007 | 89 | 14 | إن ربك لبالمرصاد |
| | | Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka. |
|
6008 | 89 | 15 | فأما الإنسان إذا ما ابتلاه ربه فأكرمه ونعمه فيقول ربي أكرمن |
| | | To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni." |
|
6009 | 89 | 16 | وأما إذا ما ابتلاه فقدر عليه رزقه فيقول ربي أهانن |
| | | Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni." |
|
6010 | 89 | 17 | كلا بل لا تكرمون اليتيم |
| | | A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya! |
|
6011 | 89 | 18 | ولا تحاضون على طعام المسكين |
| | | Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci! |
|
6012 | 89 | 19 | وتأكلون التراث أكلا لما |
| | | Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa. |
|
6013 | 89 | 20 | وتحبون المال حبا جما |
| | | Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa. |
|
6014 | 89 | 21 | كلا إذا دكت الأرض دكا دكا |
| | | A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai. |
|
6015 | 89 | 22 | وجاء ربك والملك صفا صفا |
| | | Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu. |
|