نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
6002 | 89 | 9 | وثمود الذين جابوا الصخر بالواد |
| | | Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)? |
|
6003 | 89 | 10 | وفرعون ذي الأوتاد |
| | | Da Fir'auna mai turãku. |
|
6004 | 89 | 11 | الذين طغوا في البلاد |
| | | Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa? |
|
6005 | 89 | 12 | فأكثروا فيها الفساد |
| | | Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu. |
|
6006 | 89 | 13 | فصب عليهم ربك سوط عذاب |
| | | Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba. |
|
6007 | 89 | 14 | إن ربك لبالمرصاد |
| | | Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka. |
|
6008 | 89 | 15 | فأما الإنسان إذا ما ابتلاه ربه فأكرمه ونعمه فيقول ربي أكرمن |
| | | To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni." |
|
6009 | 89 | 16 | وأما إذا ما ابتلاه فقدر عليه رزقه فيقول ربي أهانن |
| | | Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni." |
|
6010 | 89 | 17 | كلا بل لا تكرمون اليتيم |
| | | A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya! |
|
6011 | 89 | 18 | ولا تحاضون على طعام المسكين |
| | | Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci! |
|